Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC Sun bayyana cewa Jana’zar Sayyid Hassan nasarallah da kuma magajinsa Sayyid Safiyuddeen ya bayyana irin karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya.

A wani bayani wanda dakarun suka fitar sun bayyana cewa, taron da kungiyar ta gudanar na shahidan shuwagabanninta a jiya, ya tabbatar da cewa kungiyar tana da karfi kuma tana da karfin kawo karshen HKI a yankin da kuma kwato kasashen Larabawan da aka mamaye.

Rahoton ya kara da cewa a fagen kasa da kasa kuma, mutanen da suka taru ko suka yi gangami a jana’izar ya tabbatar da yadda wannan kungiyar take da karbuwa a cikin kasar a kuma kasashen duniya da dama, saboda irin yawan baki daga kasashen waje da suka halarci Jana’izar.

Rahoton ya kara da cewa kokarin da jiragen yakin HKI suka yi na tarwatsa taron a lokacinda ta getta ta kan wurin taron ya nuna karfin wannan kungiyar da kuma yadda mutane suka amince da su. Amma tare da godiyar All..babu wanda ya tanka masu a lokuta biyu da suka ratsa ta kan taron.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Zan Samar da Karin Makarantu a Zaria – Dr. Abbas Tajuddeen

Shugaban majalisar wakilai, Dr Abbas Tajuddeen ya bayyana aniyar kafa karin makarantu a Zaria.

Shugaban majalisar wakilai, Dr Abbas Tajuddeen ya ce za a kafa karin makarantu a mazabar tarayya ta zaria a kasafin kudin shekarar 2026.

Shugaban majalisar ya bayyana haka ne lokacin babban taron shekara karo na 31 da 32 na kungiyar bunkasa ilimi ta zaria, watau ZEDA da aka gudanar a Zaria.

Ya bayyana cewa makarantun da ake shirin kafa wa sun hada da makarantar firamare da sakandare na yara masu bukata ta musamman da kwalejin tarayya na koyon aikin noma da kiwo.

Shugaban majalisar ya kuma bayyana fara bada tallafi na musamman ga dalibin da ya fi kowa kwazo a fannin koyon ilimin kwamfuta da kuma dalibin da ya fi kowa nuna hazaka a bangaren makarantun sakandare dake lardin zazzau.

Abbas Tajuddeen bayan ya nuna rashin jin dadin sa bisa jinkirin da aka samu wajen biyan dalibai su 2500 kudin tallafin karatu da suke lardin zazzau,ya kuma bayyana kara yawan daliban zuwa 3000 a shekarar 2025.

Shugaban majalisar ya dora alhakin jinkirin da aka samu wajen biyan tallafin akan kaddamar da kasafin kudin shekarar 2024 inda ya bayyana cewa za a biya kudin da zarar al’amura sun daidaita.

Haka kuma ya bada sanarwar cewa zai gina wa kungiyar zeda tare da sanya kayayyaki irin na zamani a dakin taro da zai dauki kimanin mutane dubu daya.

Shugaban majalisar ta wakilai ya kara da cewa kudurin majalisar ne ganin ta bunkasa ilimi a matakin farko da inganta ilimin sakandare da na kimiyya da kawo sauyi a fannonin kirkira.

Domin haka a cewar sa zai magance matsalolin da ake fuskanta da kuma mai tasowa.

A don haka sai ya bukaci kungiyar da ta bullo da wani tsari da zai samar da yanayin baiwa malaman horo da shigar da iyaye cikin harkokin tattauna batutuwan da suka shafi ilimi.

Tun farko a jawabin sa na maraba,shugaban kwamitin tsare-tsare na kungiyar ta ZEDA, Dr Abdul Alimi Bello ya ce Kungiyar ta sami gagarumar nasara da ya nuna aniyar ta na samar da ingantaccen ilimi da bunkasa al’umma.

Ya ce cikin shekaru da dama, kungiyar ta kasance jagoran kungiyoyi masu zaman kansu a lardin zazzau da suke kula da ilimin zamani da bunkasa sana’o’in hannu.

A nashi jawabin, mai martaba Sarkin zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya bukaci kungiyar da ta yi amfani da kudaden shigar ta wajen tabbatar da samar da kyakkyawar sauyi a bangaren ilimi.

Haliru Hamza

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sharki: Takaitaccen Rayuwar Sayyid Shahid Hassan Nasarallah (r)
  • Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyararsa A Birtaniya Da Ireland Da Halartar Taron Kolin Kwamitin Sulhu Da Na Tsaro A Munich Da Na G20
  • Wakilin Jagoran Juyi A Wurin Jana’izar Sayyid: Gwgawarmaya Za Ta Ci Gaba
  • Ministan Wajen Sin Ya Yi Kiran Hadin Gwiwar Kasashen G20 Don Gina Duniya Mai Adalci Da Ci Gaba Na Bai-daya
  • Bayan Kalubalantar Ra’ayin Amurka Kan Gaza Trump Ya Ce Furucinsa Shawara Ce Kawai
  • Zan Samar da Karin Makarantu a Zaria – Dr. Abbas Tajuddeen
  • Wang Yi: Sin Za Ta Ci Gaba Da Mara Baya Ga Garambawul Na Kungiyar WTO 
  • Yake-Yaken Kasa Da Kasa Ne Suka Mamaye Taron G20 Na Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar A Afirka Ta Kudu
  • Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Jaddada Rashin Amincewarta Da Mika Kan Kasar Ga Amurka Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila