Sojojin Iran sun gwada amfani da sabbin jiragen yakin na zamani da suka kera a cikin gida, a cikin atisayen Zulfikar 1403 da ke gudana a kudancin kasar, wanda kuma ya hada rundunonin sojojin kasar daban-daban.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar atisayin na cewa sojojin sun gwada amfani da jirgin saman yaki samfurin Yak-130 a cikin atisayen.

Inda suka tabbatar da ingancinsa.

Ana gudanar da atisayen Zulfikar 1403 ne a yankin Tekun Omman da kuma wani bangare na yankin Tekun farasa daga kudancin kasar Iran.

Bugediya Janar Alireza Sheikh kakakin atisayen ya fadawa tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran kan cewa wannan bangare kadan ne daga atisayen, amma a yau sun gwada karfi da ingancin samfurin jiragen yaki yak-130 ne a karon farko kuma sun kara tabbatar da ingancisu.

Janar Sheikh ya kara da cewa wannan hotunan bidiyo da kuka ganin bangare ne na inda jirgin ya gwada korewarsa na kakkabo wani jirgi wanda ake sarrafashi daga nesa na makiya tare da amfani da garkuwan makami mai linzami samfurin MiG-29.  Sannan an ga yadda ya sami nasarar kakkabo shi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sabbin Nasarorin Rigakafi Da Warkar Da Cutar TB Na Kasar Sin Sun Kara Kuzarin Dakile Yaduwarta Duniya 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Kasashen Iran Da Katar Sun Jaddada Muhimmancin Shigar Da Dukkanin Bangarorin  Al’ummar Kasar A Cikin  Sha’anin Kasar
  • Iran, Lebanon, Iraki, Yemen sun fara atisayen hadin gwiwa na goyan bayan Gaza
  • NAJERIYA A YAU: Halin Da Matasa Suka Tsinci Kansu A Najeriya
  • Sabbin Nasarorin Rigakafi Da Warkar Da Cutar TB Na Kasar Sin Sun Kara Kuzarin Dakile Yaduwarta Duniya 
  • Duniyarmu A Yau: Ranar Qudus Ta Duniya Ta Shekara 1446
  • Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4
  • Araqchi: Har yanzu Iran ba ta mayar da amsa ga wasikar Trump kan tattaunawar nukiliya ba
  • Amurka Ta Sayi Man Jiragen Sama Fiye Da Ganga Miliyan 2 Daga Matatar Dangote A Watan Maris
  • Amurka Ta Siyo Man Jiragen Sama Fiye Da Ganga Miliyan 2 Daga Matatar Dangote
  • Iran Ta Turkiyya Sun Bukaci kasashen Musulmi Su Magance matsalar Jinkai A Kasar Palasdinu Da Aka Mamaye