Aminiya:
2025-02-25@00:40:29 GMT

Tinubu ne ya sauya ra’ayi kan ba ni muƙamin Minista — El-Rufai

Published: 25th, February 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta batun cewa Majalisar Tarayya ce ta ƙi tabbatar da shi domin zama Minista a shekarar 2023.

El-Rufai ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya sauya ra’ayi kan ba shi muƙamin duk da sun ƙulla yarjejeniya a kan hakan.

Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina

Ana iya tuna cewa, a watan Agustan 2023 ne Majalisar Dattawa ta ƙi tabbatar da El-Rufai a matsayin Minista, inda ta bayyana dalilai da suka shafi tsaron ƙasa da Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS ta ba da shawara.

Sai dai a hirarsa da gidan Talabijin na Arise a ranar Litinin, El-Rufai ya ce duk ba wannan ba ne face Shugaba Tinubu ne ya sauya shawara kan ba shi muƙamin.

A cewarsa, Shugaba Tinubu ne ya sauya masa akalar ƙudirinsa bayan shafe shekaru takwas a matsayin Gwamnan Kaduna.

“Bayan shafe shekaru takwas a matsayin Gwamnan Kaduna, ina da wasu burace-burace da na ƙudirta amma Tinubu ya nemi na bayar da gudunmawa a gwamnatinsa.

“Bayan haka ne muka ƙulla yarjejeniyar da sharaɗin cewa zai ba ni muƙamin Minista, amma daga bisani ya sauya shawara.

“Saboda haka a daina yarda da cewa Majalisar Tarayya ce ta ƙi tabbatar da ni saboda ba haka abun yake ba.

“Shugaban ƙasar ne kawai ba ya buƙata ta a gwamnatinsa saboda ya sauya shawara amma ko ma dai mene ne ba abin da ya dame ni ba ne,” in ji El-Rufai.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Tinubu ne ya sauya

এছাড়াও পড়ুন:

Bayan Kalubalantar Ra’ayin Amurka Kan Gaza Trump Ya Ce Furucinsa Shawara Ce Kawai

Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Shirinsa kan Zirin Gaza yana da kyau, amma ba zai tilasta aiwatar da shi ba, sai dai zai ci gaba da ba da shawara kawai

An gudanar da wani zaman taron koli na kasashen Larabawa a kasar Saudiyya, inda aka tattauna Shirin kalubalantar kudirin shugaban Amurka Donald Trump dangane da Gaza.

Taron tuntuba da aka gudanar bisa gayyatar yarima mai jiran gado na Saudiyya; Zaman ya tattauna ra’ayoyi kan kokarin hadin gwiwa na goyon bayan al’ummar Falasdinu.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya watsa rahoton cewa: An gudanar da taron na yau da kullun tare da halartar sarkin kasar Jordan, shugaban kasar Masar, da kuma kasashen Larabawan yankin Tekun Fasha, in ban da masarautar Oman, inda suka jaddada goyon bayan zaman shugabannin kungiyar na birnin Alkahira da zai karbar bakwancin zaman taron gaggawa na kungiyar kasashen Larabawa a farkon wata mai zuwa.

A nata bangaren, majiyoyin da aka sanar sun ce taron ya tattauna wata shawara ta Masar don mayar da martani ga shirin Trump na tilastawa Falasdinawa gudun hijira, wanda zai iya hada tallafin kudade da suka kai dala biliyan ashirin cikin shekaru uku.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Uba Sani Da NSA Ribadu Ba Abokaina Ba Ne — El-Rufai
  • Hukumar NPC Za Ta Gudanar Da Kidayar Jama’a Cikin Aminci- Shugaba Tinubu
  • Gwamnatin Iraki Ta Kokawa Sabuwar Gwamnatin Siriya Dangane Da Barazanar Mayakan Daesh Da Suka Rage A Kasar
  • Mataimakin Shugaban APC Da Mambobi 7,500 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Bauchi
  • Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano a 2023 — Ata
  • Bayan Kalubalantar Ra’ayin Amurka Kan Gaza Trump Ya Ce Furucinsa Shawara Ce Kawai
  • Na Fi Ɗaukar Noma A Matsayin Sana’a Fiye Da Waƙa -Rarara
  • Shan Maganin Fitar Da Zaƙi Kafin Haihuwa
  • Dalilan ƙara kuɗin Jami’ar Gombe — Gwamna Inuwa