Luwaɗi: An yanke wa ɗalibai biyu hukuncin bulala a bainar jama’a
Published: 25th, February 2025 GMT
Wata kotu a lardin Aceh da ke ƙasar Indonesia ta yanke wa wasu ɗalibai maza biyu hukuncin bulala a bainar jama’a.
A ranar Litinin ce kotun ta yanke wa mutanen biyu hukuncin bayan samun su da laifin luwaɗi da juna.
Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke KatsinaA yayin da mu’amala tsakanin jinsi ɗaya ta halasta a wasu yankunan ƙasar mafi rinjayen musulmi a duniya, sai ɗabi’ar ta haramta a lardin Aceh da aka ayyana dokokin shari’ar Musulunci.
Tun a watan Nuwamban bara ne dai ’yan sanda masu ɗabbaka shari’a suka kama mazajen biyu da ke karatu a wata jami’a suna aikata wannan alfasha a wani ɗaki da suka kama haya a birnin Banda Aceh.
Jami’i mai shigar da ƙara mai suna Alfian ya ce Kotun Shari’a ta Banda Aceh ta samu mutanen biyu da laifin luwaɗi kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito.
Kotun ta yanke wa ɗaya daga cikinsu bulala 85 saboda shi ne ja gaba wajen kama hayar ɗakin yayin da ta yanke wa ɗayan hukuncin bulalai 80 a cewar Alfian.
Alfian ya ce za a zartar da hukuncin yi wa ɗaliban biyu bulala gabani ko bayan watan Azumin Ramadana.
Zartar da hukuncin bulala a bainar jama’a ba sabon lamari ba ne a lardin Aceh kan laifukan da suka haɗa da caca, shan barasa ko zina.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama na adawa da hukuncin bulala a bainar jama’a da suke ɗauka a matsayin zalunci, sai dai wannan doka karɓaɓɓiya ce a wurin mazauna lardin Aceh.
A shekarar 2021 ce aka yi wa wasu ma’aurata masu auren jinsi bulala.
Haka kuma, a watan Janairun da ya gabata ne aka yi wa wasu maza huɗu bulala saboda caca a yanar gizo, hukuncin da shi ne na farko da aka zartar bana.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hukuncin bulala a bainar jama a a lardin Aceh ta yanke wa
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamishinan ‘Yansandan Kano Ya Nemi Taimakon Sarakunan Gargajiya Wajen Kawo Ƙarshen Faɗan Daba
Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata.
Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa.
Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa.
Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu.
“Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba da addabar Kano,” in ji CP Bakori.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp