Leadership News Hausa:
2025-03-28@03:20:50 GMT

Ya Kamata Trump Ya Yi Koyi Da Nixon

Published: 25th, February 2025 GMT

Ya Kamata Trump Ya Yi Koyi Da Nixon

Ranar 21 ga watan Fabrairu ne aka cika shekaru 53 da shugaban kasar Amurka na lokacin Richard Nixon ya kawo ziyara kasar Sin a shekara ta 1972, ziyarar ta sauya tarihin duniya, ta kuma samar da tushen ci gaban yankin Asiya da tekun Pasifik cikin lumana. Lokacin da tunanin yakin cacar baka ya yi kamari a Amurka, Nixon ya fahimci muhimmancin jamhuriyar jama’ar kasar Sin a ci gaban Asiya da duniya baki daya.

Nixon, ya kasance dan siyasa mai ra’ayin mazan jiya wanda ya girma cikin yakin cacar baka, amma duk da haka ya keta shingayen mulkin mallaka, danniya da babakere na wancan lokaci don fahimta da sauke alhakin da ke kansa na tarihi, ta hanyar hadin gwiwa da tuntuba, wanda ya dace shugaban Amurka mai ci Donald Trump ya yi koyi daga gare shi. Sai dai shi Trump ya zabi barazana da sa-in-sa a matsayin hanyar sadarwarsa. Karin harajin kashi 25 kan karafa da goron ruwa da Trump ya yi barazana, da karin harajin kashi 10 da ya dorawa kayayyakin kasar Sin, mataki ne da ya yi watsi da ruhin dangantaka da Nixon ya shimfida, ya kuma karya lagon alakar Amurka da Sin. Bugu da kari, da dama daga cikin sanannun “masu adawa da kasar Sin” sun samu gindin zama a gwamnatin Trump.

Duk da cewa, akwai da yawa daga cikin kalaman Trump dake nuna yakininsa na cewa zai iya “sassantawa” da kasar Sin da kuma yabon da yake yi wa shugaban kasar Sin Xi Jinping, za a iya samun wata boyayyar ajanda karkashin manufar Trump fiye da kallon kasar Sin a matsayin “kishiya ko abokiyar takara”. To, idan duk harajin da ya yi barazanar kakabawa suka fara aiki, ba shakka matakin zai yi tasiri ga tattalin arzikin kasar Sin, amma zai fi yin tasiri ga mabukatan Amurka. Wasu na ganin zai iya haifar da koma bayan tattalin arziki a duniya. Kana, zai yi matukar wahala a kai ga cimma matsaya da fahimtar juna wajen tunkarar dabaru ko wasu batutuwa masu muhimmanci a tsakanin kasashen biyu idan har aka fara gasar daukar matakan da za su illata tattalin arziki. Gaskiyar lamarin ita ce, farfado da tattalin arzikin Amurka kamar yadda Trump ya yi ikirari na bukatar karin zuba jari a ababen more rayuwa na Amurka da kuma kokarin hadin gwiwa daga bangaren gwamnatin Amurka don habaka fannin kimiyya da fasaha, sai dai kash, babu dayan wadannan da ke faruwa a halin yanzu. Maslaha mafi sauri da sauki ita ce yin aiki da kasar Sin kamar yadda Nixon ya yi, ba yin adawa da ita ba. Amma fa da Trump zai gane. (Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Trump ya yi

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Turkiyya Sun Bukaci kasashen Musulmi Su Magance matsalar Jinkai A Kasar Palasdinu Da Aka Mamaye

A zantawa ta water tarho ministocin harkokin waje na kasashen Iran da Turkiya sun bukaci kasashen musulmi su magance matsalar jinkai da kayakin agaji na Falasdinawa a kasarsu da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Hakan Fidan na kasar Turkiya da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi suna fadar haka a jiya Litinin.

A lokacinda yake Magana a kan rikicin da ke faruwa a kasar Turkiyya Abbas Aragchi ya bayyana cewa, rikici ne na cikin gida, kuma yana fatan gwamnatin kasar zara iya magancece ta yadda ta ga ya dace, kuma yana da imani zata iya magance matsalar.

Aragchi ya kara da cewa, wannan shi ne matsayin iran a cikin al-amuran da ke faruwa a kasashen yankin, ya kuma bayyana muhimmancin mutunta al-amuran da suka shafi cikin gida na ko wace kasa a yankin.

Sai kuma Hakan Fidan ministan harkokin wajen Turkiya  wanda ya sake jadda matsayin kasarsa  wajen neman hanyoyin diblomasiyya don warware matsalolin al-amuran Falasdinu da kasashen yankin da kuma sauran kasashen duniya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Sin Na Adawa Da Kara Yawan Kamfanoninta Cikin Jerin Wadanda Amurka Ta Takaita Fitar Da Kayayyakinsu
  • Karin Harajin Amurka Zai Illata Tattalin Arzikin Duniya
  • Wang Yi Ya Gana Da Takwaransa Na Faransa
  •  Kasashen Iran Da Katar Sun Jaddada Muhimmancin Shigar Da Dukkanin Bangarorin  Al’ummar Kasar A Cikin  Sha’anin Kasar
  • Ranar Kudus: al’ummar Iran zasu nuna hadin kan su ga duniya_ Pezeshkian
  • Duniyarmu A Yau: Ranar Qudus Ta Duniya Ta Shekara 1446
  • Araqchi: Har yanzu Iran ba ta mayar da amsa ga wasikar Trump kan tattaunawar nukiliya ba
  • Alamar Deepseek” Ta Bude Kofar Gyara Na Kara Kunno Kai A Harkokin Duniya
  • Iran Ta Turkiyya Sun Bukaci kasashen Musulmi Su Magance matsalar Jinkai A Kasar Palasdinu Da Aka Mamaye
  • Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDD