Kasashen Kawancen Sahel Sun Kadaddamar Da Tutar Kungiyar
Published: 25th, February 2025 GMT
Kasashen nan guda uku mambobin kungiyar kawancen Sahel (AES) da suka balle daga kungiyar ECOWAS, sun kaddamar da tutarsu ta bai daya.
An kadaddamar da tutar ne a yayin haduwar ministocin harkokin wajen kasashen jiya Asabar a Bamako babban birnin kasar Mali mai rike da shugabancin kungiyar na farko.
Firaministan Mali, Janar Abdoulaye Maïga ya bayyana a yayin bikin, cewa “Tutar kungiyar AES, launin kore, tana dauke da tambarin kungiyar a tsakiyarta.
Ya jaddada cewa launin kore yana nuna alamar bege da wadata, wanda ke wakiltar dukiya da karfin tattalin arziki.
Wannan sabuwar alamar ta kunshi hadin kai da muradin bai daya na kasashen uku, inda suka kuduri aniyar yin aiki tare domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar yankin inji shi.
Kaddamar da wannan tuta na zuwa ne kasa da wata guda bayan da aka kaddamar da fasfo din kungiyar a ranar 29 ga watan Janairun 2025, Da nufin karfafa hadin gwiwarsu da saukaka zirga-zirgar jama’a da kayayyaki cikin ‘yanci a cikin yankin.
Wannan taron, wanda wani bangare ne na taron ministocin da ke ci gaba da gudana har zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu, ya tabbatar da aniyar Mali, Burkina Faso da Nijar na kulla kawance mai karfi da ‘yanci, bayan ficewarsu daga ECOWAS da suak zarga da zama ‘yar amshin shatan kaashen yamma musamman faransa wacce ta yi musu mulin mallaka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 2 sun rasu, wani ya ji rauni a hatsarin mota a Kano
Aƙalla mutum biyu ne suka rasu, yayin da wani ya jikkata a wani hatsarin mota da ya auku kusa da Sinimar Eldorado da ke kan titin zuwa Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano.
Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar da faruwar lamarin.
Gidauniyar Daily Trust da WRAPA sun ’yanta fursunoni 21 a Kaduna da Katsina Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasuHatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:15 na safiyar yau Laraba, inda ya haɗa wata babbar mota ƙirar DAF da babur ƙirar Jincheng.
Mai magana da yawun FRSC, Abdullahi Labaran, ya ce tuƙin ganganci ne ya haddasa hatsarin.
“Daga cikin mutum shida da hatsarin ya shafa, biyu sun rasu, yayin da ɗaya ya samu munanan raunuka,” in ji shi.
Jami’an FRSC sun isa wajen da hatsarin ya auku cikin minti uku sannan suka kai wanda ya jikkata zuwa Asibitin Murtala Muhammad domin samun kulawar gaggawa.
An kuma kai gawarwakin waɗanda suka rasu Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
An miƙa motocin da sauran kayayyakin da aka ƙwato zuwa ofishin ‘yan sanda na Gwagwarwa domin ci gaba da bincike.
FRSC, ta shawarci direbobi da su bi dokokin hanya tare da yin tuƙi cikin taka-tsantsan don kaucewa irin waɗannan haɗura.