Amurka Ta Laftawa Iran Wasu Sabbin Takunkumai
Published: 25th, February 2025 GMT
Gwamnatin Trump ta saka sabbin takunkumai kan wasu mutane da ke da alaka da wani kamfanin fitar da mai na Iran.
Takunkuman sun shafi mutane 22 da jiragen ruwa 13 da ke da alaka da masana’antar mai ta Iran.
Wadannan takunkumin wani bangare ne na matsin lamba na shugaban Amurka Donald Trump kan Iran.
Ma’aikatar Baitulmali ta Amurka ta sanar da cewa, takunkumin na da nufin gurgunta harkokin hada-hadar kudi da kuma cinikin man fetur na Iran, da nufin takaita shirinta na nukiliya.
Iran dai na mai kakkausar suka kan takunkuman na Amurka, tana mai kallonsu a matsayin sabawa ka’idojin kasa da kasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi: babu tattaunawa kan batun tace sinadarin uranium
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa babu batun tattaunawa kan shirin kasar na tace sinadarin Uranium wanda ke a matsayin wani bangare na shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya.
Abbas Araghchi ya kuma ce tattaunawar Tehran da Washington ba za ta haifar da wani sakamako ba idan ana amfani da matsin mata lamba da rashin mutunta juna.
Mista Araghchi ya bayyana hakan ne a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin Iran na mako-mako a birnin Tehran babban birnin kasar, bayan da manzon musamman na Amurka Steve Witkoff ya ce Tehran “dole ne ta kawar da” shirinta na inganta makamashin nukiliya domin cimma matsaya da Washington.
Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da bangarorin ke shirin ganawa a ranar Asabar.
Da ya tabo yunkurin da Amurka ke yi na matsin lamba kan Iran a yayin shawarwarin, ministan harkokin wajen na Iran ya ce: Matsayinmu da ayyukanmu a bayyane suke, ba za su cimma komai ta hanyar matsin lamba ba, idan aka yi shawarwarin a cikin yanayi na mutuntawa, za a iya samun ci gaba, amma babu abin da za a samu ta hanyar matsin lamba ba.
Araghchi ya kuma soki “wasu batutuwa masu cin karo da juna” da ke fitowa daga gwamnatin Trump gabanin tattaunawar ta ranar Asabar.
Dama tun farko Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayatullah Khamenei ya bayyana a ranar Talata cewa tattaunawar Iran da Amurka a birnin Muscat na kasar Omani ta yi kyau a matakin farko, sai dai ya kara da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da matukar shakku ga daya bangaren.