IRGC : Jana’izar Nasrallah Wani Sakon ‘yan Gwagwarmaya A Duniya Baki Daya
Published: 25th, February 2025 GMT
Rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Iran, ta bayyana bikin jana’izar sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai rasuwa Sayyed Hassan Nasrallah da kuma Sayyed Safiedinne da aka gudanar a matsayin wani babban sako na ‘yan gwagwarmaya ga duniya baki daya.
Wannan babban taron da akayi a Beirut abun tarihi ne ga duniyar musulmi, ya kuma nuna cewa kungiyar Hizbullah, na da karfinta da kuma akidar kyamar sahyoniyawan.
Sanarwar ta kara da cewa: “Bikin da ya samu halartar miliyoyin mutane, a daidai lokacin da ake barazana da jiragen yakin Isra’ila, ya zama wata alama ta karfin Musulunci da cikakken hadin kan al’ummar kasar Labanon.
Sanarwar ta yi nuni da cewa, gagarumin taron makoki daga kasashe daban-daban, addinai da kabilu, da jam’iyyun siyasa, sun sabunta mubaya’a ga shahidan ‘yan gwagwarmayar, tare da bayar da martani mai karfi ga makiya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Daban Gwamnatin Siriya Sun Kai Farmaki Kan Masallacin ‘Yan Shi’a A Birnin Damascus
‘Yan daban sabuwar gwamnatin Siriya sun kai samame wani Masallaci da ke cikin karkarar birnin Damascus tare da korar masu ibada
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Siriya ta sanar da cewa: Jami’an tsaron kasar da ke da alaka da gwamnatin rikon kwarya a kasar Siriya sun kai farmaki kan Masallata da ‘yan kasar ke gudanar da ibadu a cikin masallacin Al-Mustafa da ke unguwar Andalusia a garin Babila a cikin karkarar birnin Damascus, bayan da suka ki mika musu makullan masallacin da kuma rufe Masallacin saboda sabanin Mazhaba.
Hakazalika ‘yan daban Al-Jolani sun lalata ofisoshi da hotuna da ke cikin masallacin, lamarin da ya fusata mazauna birnin.
Masu lura da al’amura sun bayyana cewa: An gina masallacin ne da kudade daga mabiya Ahlul-baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su), kuma ba shi da alaka a hukumance da ma’aikatar kula da harkokin Baitul-Malin addini na kasar Siriya, wanda hakan na iya zama dalilin cece-kuce kan gudanar da masallacin.