Ba ni lokacin cacar baka da El-Rufai —Nuhu Ribadu
Published: 25th, February 2025 GMT
Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ƙaryata zargin da tsohon abokinsa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi masa na neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2031.
A wata hira da aka yi da El-Rufai cikin dare ne tsohon gwamnan Kadunan ya yi zargin cewa Nuhu Ribadu yana da burin tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa.
A yayin hirar da aka yi da shi a cikin dare a kafar Arise TV ranar Litinin, El-Rufai ya bayyana cewa sun raba jiha da tsohon abokin nasa Nuhu Ribadu da kuma Gwamnan Kaduna mai ci kuma magajinsa, Sanata Uba Sani, yanzu duk ba abokansa ba ne.
Amma martaninsa, a cikin sakon da ya fitar jim kaɗan da ta tsohon gwamnan, Nuhu Ribadu ya ce, ƙarya El-Rufai yake yi cewa ya taɓa yin maganar tsayawarsa takarar 2031 da tsohon gwamnan ko da wani.
NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? Tinubu ne ya sauya ra’ayi kan ba ni muƙamin Minista — El-Rufai“Ba don kada in yi shiru a ɗauka maganar El-Rufai gaskiya ba ce, da na yi watsi da shi. Ni tulin aikin da ke gabana a yanzu ma kaɗai ya ishe ni, balle in tsaya ɓata lokaci ina cacar baka da El-Rufai ko waninsa a kafofin watsa labarai.
Martanin Nuhu Ribadu ga El-Rufai“Duk da cewa ya sha takala ta da caccaka ta, amma saboda mutunta tsohuwar abotarmu, ban taɓa fitowa na aibata shi ba, kun ba zan fara ba.
“Amma ina roƙon jama’a su yi watsi da maganganun da El-Rufai ya yi a kaina.
“Domin kawar da shakku, babu mahalukin da na taɓa magana da shi cewa zan nemi takarar shugaban ƙasa a 2031. Abun da na sa a gaba shi ne ganin Najeriya ta bunƙasa da kuma nasarar Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
“Saboda haka ina roƙon El-Rufai ya ƙyale Ni in fuskanci aikin yi wa kasa hidima da ke gabana, kamar yadda ni ma ban shiga masa harkokinsa ba.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: takarar shugaban ƙasa zaɓen 2031 El Rufai ya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Adeleke Ya Kaɗa Ƙuri’a a Zaɓen Ƙananan Hukumomin Osun
Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a faɗin jihar a ranar Asabar. Gwamnan ya isa rumfar zaɓensa da ke Sagba/Abogunde, Ƙaramar Hukumar Ede, inda aka tantance shi kafin ya kaɗa kuri’arsa.
Zaɓen, wanda ake gudanarwa don zaɓen sabbin shugabanni a ƙananan hukumomi 30 na jihar, ya samu fitowar masu zaɓe sosai tare da ingantaccen tsaro. Gwamna Adeleke ya yaba da yadda zaɓen ke tafiya cikin lumana, inda ya buƙaci al’umma su ci gaba da kaɗa ƙuri’a ba tare da tsoro ko matsin lamba ba.
Gwamnan Shekarar 2024: Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke An Yanke Wa Mutane 5 Hukuncin Kisa Bayan Sun Kashe Wani Bafullatani A Jihar OsunDa yake jawabi ga manema labarai bayan kaɗa ƙuri’arsa, ya jinjinawa hukumar zaɓe ta Jihar Osun (OSSIEC) bisa shirya ingantaccen zaɓe. Ya kuma jaddada muhimmancin dimokuraɗiyya a matakin ƙananan hukumomi, yana mai kira ga ‘yan jihar da su fito kwansu da kwarkwata domin amfani da hakkinsu na zaɓe.