Aminiya:
2025-02-25@16:35:05 GMT

Luwadi: Magijanci ya lalata dan shekara 5 a Zariya

Published: 25th, February 2025 GMT

Mutanen unguwa sun kama wani magidanci mai shekara 45 kan zargin sa da lalata wani yaro ɗan makarantar firamare ta hanyar luwadi a yankin Zariya ta Jihar Kaduna.

Al’ummar yankin sun ce dama ana zargin mutumin da yi wa yara maza fyade, don haka suke ta bibiyar motsinsa, kuma yaron ya faɗa da bakinsa cewa kusan sau uku mutmin yana ɗaukar sa.

Wanda ke zargin yana sana’ar sayar da rake ne a Bakin Dago Tudun Jukun a Karamar Hukumar Zariya Jihar Kaduna.

Aminiya ta ziyarci xibiyar da ke kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Kofar Gayan Zariya domin samun sahihin bayani kan lamarin a likitance.

Magidanci ya sari matarsa da adda har lahira Ya daɓa wa yayansa wuƙa saboda Naira 700 Luwaɗi: An yanke wa ɗalibai biyu hukuncin bulala a bainar jama’a

Manajar Cibiyar, Hajiya A’isha Ahmed ta ce a ranar 12 ga watan 2 2025 ofishin ’yan sanda da ke Gonar Ganye, gundumar Tukur Tukur ya kawo wani yaro ɗan shekara 5 kuma ɗan aji ɗaya a makarantar firamare da ake zargin mutumin da lalatawa.

Bayan likitoci sun duba sun gano cewa yaron duburarsa ta bude, wanda hakan ke nuni da an yi yunƙurin zakke masa ta duburarsa.

Hajiya A’isha Ahmed ta ce sun dora yaron a kan magani har na tsawon kwanaki 28 kuma za su rika bibiyar sa domin su tabbatar da cewa yana amfani da maganin yadda ya kamata.

Ta ci gaba da cewa za ta tura sakamakon zuwa ga Kwamishinan Lafiya na Jihar Kaduna, kuma ta tabbatar da cewa sun bai wa jami’an ’yan  sanda kwafin binciken.

Hajiya A’isha Ahmed ta yi kira ga iyaye da su daina boye irin wannan mugun abin da ke faruwa da yaransu wai don gudun abin kunya ko halin da yaran za su shiga.

Ta kara da cewa zuwa asibitin da yaran da aka ci zarafinsu a kan lokaci yana taimakawa wajen kula da lafiyarsu.

Mahaifin yaron da aka ɓata ya koka kan yadda ya ce wasu makusantan wanda ake zargin suke ƙoƙarin ɗanne shi da kuma kare shi wanda ake zargin.

Ya ce “abin mamaki shi ne ta yadda suka bi ta hannun mai anguwa wai a bani kuɗi na bar maganar,” DOn haka ya ce a shirye yake da ya bi haƙƙin ɗan nasa domin daƙile irin hakan a nan gaba ga ’ya’yan wasu.

Duk ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, ya ci tura, domin layin wayarsa ta ƙi shiga, kuma har rubutaccen sakon da aka aika masa bai amsa ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Luwadi yaro Jihar Kaduna

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Katsina Ta Kashe Naira Biliyan 5.7 Wajen Sayen Awaki 40,000 Domin Raba Wa Mata

Gwamnan ya gargadi jami’an gwamnati da su kauce wa dabi’ar nuna san kai da rashin gaskiya wajen zabo matan da za su amfana da wannan tallafi.

A cewar Gwamna Radda, an zabo mata 10 daga kowace guduma, kuma za a bai wa kowace mace awaki guda hudu da suka hada awaki uku da bunsuru daya, sannan za a bai wa kwararren manomi guda hamsin wanda zai koyar da su dubarun kiwo.

Tun da farko da take jawabi, kwaminisiyar harkokin mata ta Jihar Katsina, Hajiya Hadiza Yar’adua ta bayyana wannan tallafi a matsayin wata gagarumar gudummawa da gwamnati za ta bunkasa harkokin mata ta hanyar dogoro da kai.

A cewarta, taimakon da Gwamna Radda ya bayar ko shakka babu zai amfani mata masu sana’o’i tare bunkasa tattalin arziki a Jihar Katsina da ƙasa baki daya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Sin Ta Cimma Burin Magance Gurbatar Yanayi A Shekara Ta 2024
  • CORET Zata Ciyarda Makarantun Makiyaya Shida A Jihohin Kaduna Da Jigawa
  • Yadda jama’a suka kama ɗan shekara 65 ɗauke da bindiga
  • Ana zargin malami da azabtar da ɗalibi saboda shan mangwaro a makaranta
  • Gwamnatin Katsina Ta Kashe Naira Biliyan 5.7 Wajen Sayen Awaki 40,000 Domin Raba Wa Mata
  • Masu Kira ta Waya a Shirin FRCN Kaduna Sun Koka Kan Jinkirin Biyan Fansho
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Taya Gwamna Bago Murnar Cika Shekara 51
  • Za a kafa ƙarin makarantu a Zariya — Abbas Tajudeen
  • Ɗan shekara 43 ya auri mai shekara 88