Mutum 7,000 Suka Mutu A Rikicin Gabashin Kwango Tun Daga Watan Janairu
Published: 25th, February 2025 GMT
Fiye da mutane 7,000 da yawancinsu fararen hula ne aka kashe a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango tun daga watan Janairu, in ji Firaminista Judith Suminwa Tuluka a ranar Litinin.
Mambobin kungiyar M23 da ke samun goyon bayan kasar Rwanda sun kwace iko da yankunan gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo masu arzikin ma’adinai da suka hada da manyan biranen Goma da Bukavu da ke gabashin kasar.
Firayim Minista Judith Suminwa Tuluka ta yi gargadin cewa, halin da ake ciki na tsaro a gabashin DRC ya kai matsayi mai daukar hankali, yayin da take jawabi ga kwamitin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva.
Ta ce mutanen da suka mutu sun hada da “fiye da gawarwaki 2,500 da aka binne ba a san ko su waye ba” kuma gawarwakin mutane 1,500 na nan a dakin ajiye gawa.
A cewar rahotannin Majalisar Dinkin Duniya, ‘yan kungiyar M23 dauke da makamai, wadanda ke samun goyon bayan sojojin Rwanda kimanin 4,000, suyka abkawa yankunan, lamarin da ya tilastawa dubban mutane tserewa daga yankin.
A baya-bayan nan ne dakarun M23 suka karbe iko da Bukavu, babban birnin lardin Kivu ta Kudu, bayan da suka kwace Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa.
Firayim Ministan Kongo ya ce an kashe fiye da mutane 3,000 a Goma kadai.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato
’Yan bindiga sun kashe mutane arba’in a wani hari suka kai a ƙauyen Zike, a yankin Kwall da ke Ƙaramar Hukumar Bassa a Jihar Filato.
Wani shugaban al’ummar Kwall, Wakili Tongwe, ya ce maharan sun shiga ƙauyen ne da sanyin safiyar ranar Litinin suna harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya sa mazauna gujegujen neman tsira.
Ya shaida wa wa kafar talabijin ta Channels cewa wata tawagar ’yan banga, da shi kansa da wasu jami’an tsaro, suna sintiri a wani ƙauye ne lokacin da maharan suka kai harin.
Ko da yake jami’an tsaron sun yi artabu da maharan kuma sun yi nasarar fatattakar su, amma an riga an riga an kashe mutane talatin da shida nan take, wasu huɗu kuma suka mutu daga baya.
Boko Haram ta kashe mutum 300 ta kwace ƙananan hukumomi 3 a Borno — Ndume NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar BornoWasu mazauna garin kuma sun samu raunukan harbin bindiga kuma suna samun kulawa a asibiti.
Hukumomin tsaro a jihar ba su yi wani sharhi ba game da harin, wanda ya zo ƙasa da makonni biyu bayan an kashe mutane hamsin da biyu a wasu ƙauyukan Karamar Hukumar Bokkos ta Jihar.