Dan kwallon Najeriya ya mutu bayan fadowa daga bene a Uganda
Published: 25th, February 2025 GMT
Wani dan kwallon Najeriya mai suna Abubakar Lawal daga Jihar Sakkwato ya rasu bayan fadowa daga bane a kasar Uganda, inda yake taka leda.
Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar Lawal mai shekaru 29 ya gamu da ajalinsa ne bayan ya fado daga hawa na uku na wanin babban kantin sayar da kayayyaki a Kampala, babban birnin kasar Uganda.
Rasuwar tasa ta haifar haifar da ce-ce-ku-ce a kasar, kamar yadda kafofin yada labarai suka ruwaito. Da farko an alakanta rasuwar tasa da hatsarin babur, kafin daga bisani jami’an tsaro su bayyana cewa ya fado ne daga bene.
Marigayin dan wasan gaba ne a kungiyar kwallon kafa ta Vipers da ke kasar, inda ya fara wasa tun shekara 2022, kafin nan ya shekara biyu yana taka lelda a kungiyar AS Kigali da ke kasar Rwanda.
Kungiyar Vipers ta sanar Abubakar ya rasu ne a ranar Litinin bayan da ya fado daga hawa na uku da kataferen kantin mai suna Voicemall Shopping Arcade a Kampala.
A sakon ta’aziyyarta, kungiyar ta bayyaan marigayin a matsayin, “mutumin kirki mai kyakkyawar zuciya, mai yawan kyauta ne da kuma taimaka wa jama’a,” kamar yadda ya wallafa a shafinta na X.
Runudar ’yan sandan ta sanar da fara bincike kan musabbabin mutuwar dan kwallon na Najeriya.
Hukumar ’yan sandan Uganda ta bayyana cewa dan wasan ya gamu da ajalinsa ne a lokain da ya kai wa wata kawarsa ’yar kasar Tanzaniya ziyara a rukunin ginin.
A sakon ta’aziyyar dan wasan, kungiyar Nasarawa United, tsohuwar kungiyar Abubakar, ta ce, “Muna jimaminin mutuwar fuju’ar tsohon dan wasanmu Abubakar Lawal, kuma muna rokon Allah Ya sada shi da rahama.”
Shi kuwa Mustafa Kizza, dan wasan Uganda, ya ce: “Rashin Lawal abu ne mai wuyar jurewa. Mutumin kirki ne mai fara da hazaka da ba za mu taba mantawa da shi ba.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun ceto mafiya 16 da aka yi garkuwa da wasu a Filato
Sojoji a Jihar Filato sun ceto wasu mutum 16 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan titin Jos zuwa Mangu.
Dakarun Rundunar Operation Safe Haven ne suka ceto mutanen a cikin wata mota da a aka jefar da ita a yankin Mararabar Kantoma da ke Ƙaramar Hukumar Manngu.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Manjo Samson Zakhom, ya bayyana cewa an ceto mutanen ne da misalin ƙarfe 9 na dare bayan sun tsinci motar a daji babu kowa a ciki.
Ya ce ganin haka ne sojojin rundunar da ke aikin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar suka yi zargin sace fasinjojin cikinta aka yi.
An yi garkuwa da masu ibada a Kogi Yadda kisan mutum fiye da 50 a Filato ya tayar da ƙura NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar FilatoManjo Samson Zakhom ya ce sojojin suna tsaka da bincike sai ’yan bindigar suka buɗe musu wuta, inda bayan arangamar ɓata-garin suka tsere suka bar matafiyan.
Ya bayyana cewa, a cikin fasinjojin 16 da aka ceto har da ƙananan yara guda shida, kuma duk a ba sau taimakon farko saboda raunukan da suka samu, sannan muka raka su, suka ci gaba tafiyarsu.”