An Yi Ganawa A Tsakanin Ammar Hakim Na Iraki Da Shugaban Kasar Masar Abdufttah Al-Sisi
Published: 25th, February 2025 GMT
Shugaban kungiyar ‘al-Hikimah” na kasar Iraki Ammar Hakim ya gana da shugaban kasar Masar Abdulfattah al-sisi. A yayin ganawar Ammar Hakim ya jaddada muhimmancin taimaka wa kokarin da Masar take yi na ganin an hana korar falasdinawa daga yankunansu zuwa wajen Falasdinu.
Ammar Hakim ya kuma ce, a yayin wannan ganawar na bayyana wa shugaban kasar jinjinawarmu akan yadda Masar ta kasance mai taimaka wa Falasdinawa.
Haka nan kuma mun nuna goyon bayanmu ga kokarin Masar al’umma da gwamnati na hana tilasatawa Falasdinawa yin hijira da kuma kare hakkokin Falasdinawa da riko da kasarsu.
Har ila yau Ammar Hakim ya ce ganawar tasu ta tabo batutuwa da su ka shafi halin da ake ciki a wannan yankin da kuma wajabcin aiki a tsagaita wutar yaki a yankin Gaza.
Sayyid Ammar Hakim ya kuma yi ishara da muhimmanci sake gina yankin na Gaza ba tare da an fitar da mazaunansa daga ciki ba. Bugu da kari bangarorin biyu sun jaddada muhimmanci kafawa Falasdinawa daularsu akan iyakokin 1967 da birnin Kudus zai zama babban birninta domin haka ne hanyar samar da zaman lafiya a cikin wannan yankin.
Akan halin da ake ciki a matakin wannan yankin kuwa, Sayyid Ammar Hakim ya ce; Kasar Iraki tana son ganin an sami zaman lafiya a cikin wannan yankin da kuma warware sabanin da ake ciki a wannan yankin da kusanto da fahimtar juna a tsanakin bangarori mabanbanta.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Ammar Hakim ya wannan yankin
এছাড়াও পড়ুন:
Brice Ologui Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Gaban Da Kashi 90.35% A Jiya Lahadi
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda kuma ya jagoranci juyin mulkin da aka yiwa Ali Bongo tsahon shugaban kasar ya lashe zaben da aka gudanar a jiya Lahadi tsakanin yan takara 7 har da shi.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News” ya bayyana cewa Oligui dan shekara 50 a duniya, shi ne babban dogarin sojoji masu tsare fadar shugaban kasar Gaban, a lokacinda ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin da yan gidan Bogo suka yi na shekaru kimani 50 a kasar.
Labarin ya kara da cewa kashi 2/3 na mutanen Gabon wadanda yawansu bai fi miliyon 2.3 ba suna cikin talauci a cikin kasa wacce take da arziki mai yawa.
Brice zai jagoranci kasar na tsawon shekaru 7 masu zuwa kuma yana iya sake shi takarar shugabancin kasa karo na biyu.
Yan takara 6 ne suka tsaya tare da Brice amma mai binsa bai sami fiye da kashi 3 % na kuri’un da aka kada ba sannan yawan fitowar mutane masu zabe ya kai kashi 70.4% wanda ya nuna cewa an sami sauyi babban a cikin harkokin siyasar kasar ta Gabaon.