HKI: Hamas Ta Sake Gina Kanta A Arewacin Gaza
Published: 25th, February 2025 GMT
Kafafen watsa labarun HKi sun ambato jami’an soja na cewa, mayakan Hamas sun sake gina kansu ta hanyar daukar dubban mayaka, kuma suna nan a arewacin Gaza ba su fita daga ciki ba.
Kafafen watsa labarun na HKI sun kuma kara da cewa; mayakan da kungiyar take da su a yanzu, sun rubanya mayakanta na baya, kafin barkewar yaki, kuma kungiyar ta koyi darussa daga yaki da sojan kasa na Isra’ila a baya.
Jaridar “Badiot Ahranot” wacce ta dauki labarin ta kuma ce; Har yanzu Hamas ba ta fito da dukkanin mayakanta a filin daga ba, da adadinsu ya kai 30,000, kuma tana ba su albashi ta hanyar kudaden harajin da take karba.
Wani sashen na bayanin kafafen watsa labarun ‘yan sahayoniyar ya kunshi cewa; Hamas ta sake dawo da harkokin tafiyar da sha’anin yankin na Gaza domin sake gina karfinta na soja da tattalin arziki.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Bayan Kalubalantar Ra’ayin Amurka Kan Gaza Trump Ya Ce Furucinsa Shawara Ce Kawai
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Shirinsa kan Zirin Gaza yana da kyau, amma ba zai tilasta aiwatar da shi ba, sai dai zai ci gaba da ba da shawara kawai
An gudanar da wani zaman taron koli na kasashen Larabawa a kasar Saudiyya, inda aka tattauna Shirin kalubalantar kudirin shugaban Amurka Donald Trump dangane da Gaza.
Taron tuntuba da aka gudanar bisa gayyatar yarima mai jiran gado na Saudiyya; Zaman ya tattauna ra’ayoyi kan kokarin hadin gwiwa na goyon bayan al’ummar Falasdinu.
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya watsa rahoton cewa: An gudanar da taron na yau da kullun tare da halartar sarkin kasar Jordan, shugaban kasar Masar, da kuma kasashen Larabawan yankin Tekun Fasha, in ban da masarautar Oman, inda suka jaddada goyon bayan zaman shugabannin kungiyar na birnin Alkahira da zai karbar bakwancin zaman taron gaggawa na kungiyar kasashen Larabawa a farkon wata mai zuwa.
A nata bangaren, majiyoyin da aka sanar sun ce taron ya tattauna wata shawara ta Masar don mayar da martani ga shirin Trump na tilastawa Falasdinawa gudun hijira, wanda zai iya hada tallafin kudade da suka kai dala biliyan ashirin cikin shekaru uku.