Fizishkiyan: Ba Za Mu Zauna Kan Teburin Tattaunawa Da Wanda Yake Yi Mana Barazana Ba
Published: 25th, February 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi mu zauna kan teburin tattaunawa da mutumin da yake fitowa fili yana yi mana barazana, kuma ya sa hannunsa a wuyansa ya sheke mu.
Shugaban kasar ta Iran wanda ya gana da ‘yan majalisa masu wakiltar gundunar Hamadan a daren jiya Litinin ya ce; Mu mutane ne da mu ka yarda da tattaunawa,kuma a halin yanzu abinda ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yake yi kenan da kasashen makwabta.
Da ya tabo batun takunkuman da Amurka take kakaba wa Iran kuwa, shugaban kasar ta Iran ya ce, babu yadda za a yi a kakaba takunkumin ya yi tasiri akan kasar da take da iyaka mai tsawo da kasashe masu yawa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jagoran Juyin Musulunci Ya Amince Da Yin Afuwa Ga Wasu Fursunoni Masu Yawa
Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya amince da bukatar ma’aikatar shari’a na yin afuwa ga wasu fursunoni sannan kuma da rage yawan shekarun wasu na zaman gidan kurkuku.
Yin afuwar ga fursunonin dai ya zo saboda shiga sabuwar shekarar hijira shamshiyya ta 1404 da kuma karatowar karamar salla ra 1446. Bugu da kari a wannan tsakanin ne ake bikin kafa tsarin jamhuriyar Musulunci na Iran.
Shugaban ma’aikatar shari’a ta Iran Hujjatul-Islam Wal Muslimin Gulam Muhsin Eji ne ya gabatar da bukatar neman afuwar ga fursunonin ta mutane 1526, wanda kuma ya sami amincewar jagoran.
A kowace shekara a lokutan bukukuwan addini da nasa ana yi wa fursunoni masu kananan laufuka afuwa, yayin da ake rage wa wasu tsawon wa’adin zamansu a gidan kurkuku.