40% na matan Kano sun fuskaci cin zarafi a gida —Shugaban Majalisa
Published: 25th, February 2025 GMT
Shugaban Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, ya bayyana cewa mutum hudu a cikin kowane mata 10 a Jihar Kano sun fuskanci cin zarafi a gidajensu.
Tajuddeen Abbas ya bayyana cewa akalla kashi 35 na matan Najeriya sun fuskanci cin zarafi, lamarin da ya ce ya fi muni a yankin Arewa maso Yamma.
Ya bayyana wa taron wayar da kai game da illar ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma cin zarafi a cikin gidaje cewa, “abin ya fi muni a yankin Arewa maso Yamma, inda a Jihar Kano matan da ake cin zarafinsu a cikin gidajensu sun kai kashi 40 cikin 100.
Game da yawa masu ta’mmali da miyagun kwayoyi kuwa, Shugaban Majalisar Wakilan, wanda dan yankin ne, ya bayyana cewa an samu karuwar kashi 25 cikin 100 na masu ta’ammali da miyagun kwayoyi a cikin shekaru uku da suka gabata.
Dan kwallon Najeriya ya mutu bayan fadowa daga bene a Uganda Luwadi: Magijanci ya lalata dan shekara 5 a Zariya Ya daɓa wa yayansa wuƙa saboda Naira 700Tajudden mai wakiltar Zariya da Sabon Gari daga Jihar Kaduna, ya bayyana cewa an samu karuwar miyagun kwayoyi da jami’an tsaro suka kwace da kashi 28 cikin 100 a shekarar 2023.
Don haka ya yi kira da a dauki kwararan matakan gaggawa da kuma dabaru na musamman domin magance matsalolin cin zarafi a gidajen aure da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi a yankin na Arewa maso Yammak.
Ya jaddada muhimmancin hadin kan hukumomin gwamnati da da shugabannin al’umma da kungiyoyi masu zaman kansu wajen yi wa tufkar hanci.
A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Birgediya-Janar Mohamed Buba Marwa (murabsu), ya bayyan cewa a halin yanzu, daya a cikin kowane mutum hudu masu ta’ammali da miyagun kwayoyi na Najeriya, mace ce.
Buba Marwa ya c,e “mutum miliyan uku ne miyagun kwayoyi suka yi wa illa a yankin Arewa maso Yamma, daga cikin mutum miliyan 14.3 ’yan shekaru 15 zuwa 64 da ke ta’ammali da miyagun kwayoyi a Najierya.”
Amma ya ce hukumar tana kara matsa kaimi wajen yakar matsalar, inda a shekara hudu da suka gabata ta kama mutum 57,792 tare da kwale kilogram milyan 9.9 na miyagun kwayoyi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: cin zarafi Miyagun Kwayoyi ta ammali da miyagun kwayoyi ya bayyana cewa cin zarafi a
এছাড়াও পড়ুন:
UNRWA : hana shigar da kayan agaji Gaza, ya jefa yankin cikin matsanancin hali
Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ya yi gargadin cewa hana shigar da kayayyakin jin kai da Isra’ila ta yi a zirin Gaza ya jefa yankin cikin mawuyacin hali na rashin abinci.
“Makonni uku kenan da hukumomin Isra’ila suka hana shigar da kayayyaki cikin Gaza.
“Ba abinci, ba magani, ba ruwa, babu man fetur,” inji Philippe Lazzarini a cikin wani sako a shafukan sada zumunta.
Tun a ranar 4 ga watan Maris ne Isra’ila ta hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza, bayan karewar kashi na farko na tsagaita bude wuta a yarjejeniyar da ta cimma da kungiyar gwagwarmayar falasdianwa ta Hamas data kunshi musayar fursunoni tsakanin bangarorin.
Lazzarini ya jaddada cewa al’ummar Gaza sun dogara ne kan shigo da kayayyaki daga yankunan da aka mamaye.
“Duk ranar da ta wuce ba tare da agajin jin kai ba, hakan na nufin yara da yawa suna kwana da yunwa, cututtuka na yaduwa,” in ji babban jami’in UNRWA.
Lazzarini ya bayyana haramcin taimakon a matsayin wani hukuncin bai daya ga al’ummar Gaza, wadanda akasarinsu kananan yara ne da mata.
Ya yi kira da a dage wannan kawanya da kuma kai agajin jin kai da kayayyakin kasuwanci zuwa Gaza.