Aminiya:
2025-03-28@07:14:13 GMT

Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS

Published: 25th, February 2025 GMT

Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce tattalin arzikin ƙasar ya haɓaka da kaso 3.84 cikin 100 a zango na 4 na shekarar 2024.

A cewar rahoton da hukumar NBS ta fitar a yau Talata, bunƙasar ta ɗara kaso 3.46 da aka samu a zango na 3 na 2024.

An naɗa Obasanjo mai shiga tsakani a rikicin Kongo Manoman tumatir na tafka asara saboda faɗuwar farashi

Alƙaluman game da zango na 4 na shekarar 2024 sun kuma ɗara kaso 3.

46 cikin 100 da aka ba da rahoton samu a zango na 4 na 2023.

“Ɓangaren ayyuka ne kan gaba a bunƙasar ta zango na 4 na 2024, wanda ya ƙaru da kaso 5.37 cikin 100 tare da ba da gudunmawar kaso 57.38 cikin 100 na jimillar tattalin arzikin,” a cewar NBS.

A jimillar ƙididdigar shekarar ta 2024, tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka ne da kashi 3.40 idan aka kwatanta da kashi 2.74 a 2023.

Sai dai duk da haka, haɓakar ba ta cimma alƙawarin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na haɓaka tattalin arziƙin ƙasar da kashi 6 ba a shekarar ta 2024.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Nijeriya Tattalin Arziki tattalin arzikin

এছাড়াও পড়ুন:

Za mu ɗauko hayar sojojin ƙetare domin horas da dakarun Nijeriya — Badaru

Za a ɗauko hayar ƙwararrun sojoji daga ƙetare domin horar da sojin ƙasar aikin ƙundumbala wajen tunkarar ’yan ta’adda da kuma ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su a Nijeriya.

Ministan Tsaron Nijeriya, Badaru Abubakar ya sanar da haka lokacin ƙaddamar da aikin horar da sojojin 800 a Jaji da ke Jihar Kaduna.

Gaskiyar abin da ake faɗa kan ’yan fim — Samira Sani Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDD

Abubakar ya ce baya ga horaswar, gwamnati za ta samar wa dakarun kayan aiki na zamani da za su yi amfani da su wajen daƙile matsalolin tsaron da ake samu.

Ministan ya ce a karon farko, sojojin 800 za su ci gajiyar wannan horaswar, yayin da daga bisani wasu 800 kuma su biyo baya.

Badaru ya ce sun ɗauki wannan matakin ne domin tinkarar matsalar ƴan ta’adda waɗanda su ma ke sauya dabaru a kodayaushe.

Kodayake ministan bai sanar da sunayen ƙasashen da za a ɗauka hayar waɗannan zaratan sojojin ba, amma ya ce za a ɗauko su ne daga wasu ƙasashen duniya bakwai.

A zangon farko kaɗai, jimillar sojojin Nijeriya dubu 2 da 400 ne za a fara bai wa horan na musamman, kafin a tsallaka zuwa zango na biyu.

Ministan ya bayyana cewa, ana samun kwanciyar hankali a wasu yankunan ƙasar sakamakon yadda gwamnati ta duƙufa wajen magance matsalar tsaro, inda har ya ba da misali da yankin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna, yankin da a cewarsa, an samu zaman lafiya a yanzu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da matsalar ’yan bindiga musamman a yankin arewacin Najeriya, inda suke garkuwa da jama’a domin karɓar kuɗin fansa, yayin da a wasu lokuta suke aiwatar da kisa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ina Mafita Game Da Ƙalubalen Ƙarancin Abinci A Nijeriya
  • Karin Harajin Amurka Zai Illata Tattalin Arzikin Duniya
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Hana Baƙin Haure Shigowa Nijeriya Ba Bisa Ƙa’ida Ba
  • Kwalara Ta Kashe Mutum 14, Ana Zargin 886 Sun Kamu A Nijeriya – NCDC
  • Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago
  • Sin Na Ci Gaba Da Kasancewa Cibiyar Rarraba Hajojin Da Masana’antu Ke Sarrafawa
  • Kofin Duniya: Nijeriya Na Tsaka Mai Wuya
  • Kamfanin BYD Ya Samu Karin Ribar Kaso 34 Zuwa Dala Biliyan 5.6 A Bara
  • Nijeriyar Jiya Da Yau: Kiki-Kakar Sabgar ‘Yan Majalisu
  • Za mu ɗauko hayar sojojin ƙetare domin horas da dakarun Nijeriya — Badaru