Mutum 10 sun mutu a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri
Published: 25th, February 2025 GMT
An tabbatar da mutuwar mutum 10 a sakamakon wani haɗari da ya auku a babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a Jihar Yobe.
Haɗarin wanda ya jikkata mutum uku ya auku ne shingen binciken ababen hawa da jami’an tsaro suka kafa a daidai garin Warsala.
Babu hannun Naira Marley a mutuwar Mohbad — Kotu Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS
Bayanai sun ce haɗarin ya auku ne yayin da wata motar dakon kaya maƙare da siminti ta yi ƙundumbala ta faɗa wani rami.
Wata majiya ta ce fasinjoji 13 ne a cikin motar wanda 10 daga ciki suka mutu nan take yayin da ragowar ukun suka jikkata..
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce an kai waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Ƙwararru da ke Damaturu domin ba su kulawar gaggawa.
A cewarsa, binciken da aka gudanar ya gano cewa tsinkewar birki ne ya haddasa aukuwar haɗarin wanda kuma ya haɗa da wata ƙaramar mota ƙirar Sharon.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Haɗari Jihar Yobe
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar NPC Za Ta Gudanar Da Kidayar Jama’a Cikin Aminci- Shugaba Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ta dauki wani muhimmin mataki na gudanar da kidayar jama’a da gidaje da aka jima ba a yi ba, inda ya tabbatar da cewa za a gudanar da aikin cikin inganci ta hanyar amfani da fasahar zamani.
Shugaban ya ba da wannan tabbacin ne a wata ganawa da ya yi da jami’an hukumar kula da yawan jama’a ta kasa (NPC) a fadar gwamnati, shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin kidayar jama’a ga tsare-tsare na kasa, tare da jaddada aniyarsa na tabbatar da tattara bayanai masu inganci.
Shugaba Tinubu ya bayyana shirin kafa kwamitin da zai duba kasafin kidayar jama’a da kuma gano hanyoyin samun kudade.
Ya kuma jaddada bukatar hukumar kula da tantance ‘yan kasa (NIMC) ta taka rawar gani wajen gudanar da wannan aiki, tare da tabbatar da samar da ingantattun na’urorin tantancewa da suka hada da tantance fuska da murya.
Shugaban ya bayyana cewa ingantattun bayanan za su haɓaka shirye-shiryen gwamnati, musamman a fannin aikin gona da walwalar jama’a.
Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya tabbatar da kudurin na Tinubu, inda ya bayyana cewa rashin kudi ne ya janyo tsaikon kidayar jama’a.
Ya kuma bayyana cewa, NPC ta riga ta kammala muhimman ayyukan shirye-shirye da suka hada da kidayar jama’a, sannan kuma hukumomin tantancewa da kididdiga daban-daban kamar su NPC, NIMC, NBS, da Ma’aikatar Tattalin Arziki, suna aiki tare don inganta bayanan da ake da su.
Daga Bello Wakili