Hukumar JSPCACC Ta Kwato Kudaden Gwamnati Sama Da Naira Miliyan 300
Published: 25th, February 2025 GMT
Gwamnatin jihar Jigawa ta nemi hadin kan al’umma don gina kasa bisa gaskiya da rikon amana, tare da kaucewa cin hanci da rashawa ba.
Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin bude taron wayar da kan jama’a na yini 3 da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (JSPCACC) ta shirya a Dutse.
Malam Umar Namadi ya bayyana cewa, taron na da nufin wayar da kan manyan jami’an gwamnati kan ayyukan hukumar da sauran batutuwan da suka shafi hakan.
“Wannan shiri yana da matukar muhimmanci idan aka yi la’akari da yadda gwamnati ta jajirce wajen ci gaba da inganta dukkan ka’idojin gudanar da mulki.”
Gwamna Namadi ya ce, cin hanci da rashawa al’ada ce da ta yadu da ke wargaza al’umma, da cibiyoyin gwamnati.
Ya yi nuni da cewa, shugabanci nagari wanda ya hada da kaucewa rikon sakainar kashi da kin bin son zuciya, sgi ne hanya daya tilo ta yaki da talauci, da ci gaban al’umma cikin sauri, da samar da sauye-sauye masu kyau a cikin al’umma.
Ya ce, ingantaccen tsarin mulki, wanda ke tattare da rikon amana da gaskiya, shi ne tabbacin samun nasara a yakin da ake da talauci, da saurin ci gaban tattalin arziki, da sauye-sauye a tsakanin al’umma.
Namadi wanda ya bayyana gagarumin ci gaban da hukumar ta samu tun bayan kafa ta a shekarar 2022, ya bayyana cewa, ta kwato sama da naira miliyan 300 na kudaden gwamnati, tare da warware kusan rabin korafe-korafe 200 da aka samu, kuma a halin yanzu ta gurfanar da wasu kararraki 16.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
KADGIS Ta Samar Da Sabuwar Manhajar Biyan Diyyar Filaye A Kaduna
Gwamna Uba Sani ya amince da sabon tsarin biyan diyya ta hanyar amfani da fasahar zamani ga Hukumar Kula da Bayanan Filaye ta Kaduna (KADGIS), da nufin dakile almundahana a harkokin biyan diyya na filaye a fadin jihar.
Daraktan Hukumar KADGIS Dr. Bashir Garba Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin mambobin Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa (NUJ), rashen Rediyon Najeriya Kaduna, a ofishinsa da ke Kaduna.
Dr. Bashir Garba Ibrahim ya bayyana cewa wannan sabuwar manhaja za ta rika adana bayanan masu asalin filayen da za a biya diyya, da suka hada da daukar hoton ‘yan yatsun da lambar katinsu na dan kasa NIN, domin hana masu zamba karbar diyya akan filayen da ba nasu ba ne.
Haka zalika, Daraktan ya yi bayanin sauye-sauye da aka aiwatar a karkashin jagorancinsa tun bayan hawansa kan mukami.
Ya ce cikin shekaru biyu da suka gabata, KADGIS ta warware sama da kararrakin rikicin fili 700, tare da kaddamar da tsarin rangwamen kashi 20 bisa 100 ga wadanda suka biya dukkan bashin da ke kansu gaba daya, wanda hakan ya inganta samun kudaden shiga da inganta ayyuka matuka.
Dr. Bashir Garba ya tabbatar da cewa yanzu takardar mallakar fili (Certificate of Occupancy – C of O) tana cikin tsarin gaggawa, inda ake iya fitar da ita cikin sa’o’i 24 muddin dukkan sharudda sun cika, inda ake iya bayar da takardun shaidar mallakar sama da 200 a kowane mako.
A nasa jawabin, Shugaban NUJ reshen Rediyon Najeriya Kaduna, Umar Adamu S. Fada, ya yaba wa Daraktan da dukkan ma’aikatan hukumar bisa wadannan sauye-sauye, musamman na sabuwar manhajar biyan diyya, da kuma hanzarta fitar da takardun shaidar mallaka.
Ya nuna farin ciki da damar hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu, tare da bayyana shirin kungiyar na yin aiki tare da sashen hulda da jama’a na hukumar domin inganta samar da bayanai.
Kungiyar ta kuma yi tayin tallafawa hukumar, ta hanyar amfani da shirye-shiryen tasharsu don kara kusantar da jama’a ga ayyukan hukumar, da kara fadakar da su kan harkokin filaye a fadin jihar.
Umar S. Fada