Gwamnatin Neja Ta Haramta Karbar Haraji A Hannun Masu Kananan Sana’o’i
Published: 26th, February 2025 GMT
Gwamnatin jihar Neja ta haramta wa masu tattara kudaden shiga a fadin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar karbar haraji daga hannun ‘yan talla da masu kananan sana’o’i.
Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati Minna, babban birnin jihar.
Mohammed Umar Bago wanda ya yi Allah-wadai da yadda ake karbar kudade ba bisa ka’ida ba a hannun kananan ‘yan kasuwa, ya umurci shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da su kara sa ido tare da tabbatar da ganin an kawo karshen irin wadannan ayyuka nan take.
Ya tunatar da su cewa gwamnatin jihar Neja tana da tsarin bai daya da ya hana karbar haraji dafa masu kananan sana’o’i domin basu damar dogaro da kai.
“Mun yanke shawarar cewa daga yanzu, babu wwanimai karamar sana’a da za a sake karbar haraji a hannunsa a wannan jihar.”
“’Yan talla da kananan ‘yan kasuwa ba sa biyan haraji a Jihar Neja, kuma duk wanda aka samu yana karbar haraji daga wurinsu zai dandana kudarsa,” inji Gwamnan.
Daga Aliyu Lawal
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: KASUWANCI karbar haraji
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan Najeriya
Majalisar Dattawa, ta buƙaci Ma’aikatar Sadarwa da ta yi aiki tare da kamfanonin sadarwa domin rage kuɗin data, ta yadda kowa zai iya samun Intanet mai sauƙi a Najeriya.
A zaman majalisar na ranar Laraba, Sanata Asuquo Ekpenyong (APC – Kuros Riba), ya nuna damuwa kan yadda farashin data ya ƙaru da kusan kashi 200.
Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Kakakin ’yan sandan Taraba, Abdullahi Usman, ya rasuYa ce ƙarin yana hana mutane da dama musamman matasa, samun damar amfani da Intanet.
“Ƙarin farashin data ba wai kawai yana hana mutane shiga Intanet ba ne, har ma yana wahalar da matasa ’yan kasuwa da masu aiki daga gida,” in ji Sanata Ekpenyong.
Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya jaddada cewa samun Intanet mai arha zai taimaka wa ƙananan ’yan kasuwa da tattalin arziƙin ƙasa gaba ɗaya.
Majalisar ta buƙaci gwamnati da ta tsara manufofi da za su tabbatar da farashi mai sauƙi, tare da kafa cibiyoyin fasaha masu rangwame ga ɗalibai, ’yan kasuwa, da masu aiki da fasahar zamani.
Haka kuma, ta umarci Kwamitin Sadarwa na majalisa da ya binciki dalilan tashin farashin data tare da nemo mafita mai ɗorewa.