Biyo bayan umarnin da hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta bayar, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta kara wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025.

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a yau yayin taron bita ga  ma’aikata da jami’an Alhazai na kananan hukumomi a Otal din Grand Central.

Alhaji Danbappa ya bayyana cewa za a ci gaba da karbar kudaden  maniyyata har zuwa ranar daya ga watan Ramadan.

Ya kuma bayyana cewa, ya zuwa yau 25 ga watan Fabrairun 2025, hukumar ta bada sama da naira biliyan 22 ga hukumar alhazai ta kasa a madadin Alhazan jihar Kano.

Bugu da kari, babban daraktan ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa gaugawar daukar mataki na magance bukatun hukumar a duk lokacin da ake bukata.

A nasa jawabin shugaban hukumar gudanarwar Alhaji Yusif Lawan ya bukaci ma’aikata da jami’an  Alhazai na kananan hukumomi da su kara himma wajen gudanar da ayyukansu.

 

Abdullahi Jalaluddeen

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Kara Wa adin Biyan Kudi

এছাড়াও পড়ুন:

Hajj 2025: NAHCON Ta Rage N54bn Daga Kudaden Cajin Maniyyata

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar maniyyata zuwa Hajjin 2025 a Ƙasar Saudiyya har bayan Azumin Ramadan.

Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja.

Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa an rage naira biliyan 54 daga kudaden da masu ruwa da tsaki ke caji domin saukaka wa maniyyata wajen biyan kuɗin tafiya.

Ya tabbatar da cewa ana duba sabbin hanyoyin inganta muhimman ayyuka kamar abinci, masauki, da kula da lafiyar alhazai yayin da suke ƙasa mai tsarki.

A cewarsa, hukumar za ta ɗauki nauyin kuɗin tafiyar ƙwararrun masu dafa abinci 60 da za su sa ido kan shirye-shiryen abinci a wuraren da aka tanada, sakamakon korafe-korafen matsaloli da aka fuskanta a shekarar da ta gabata.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Nemi Hadin Kan Al’ummar Jihar Jigawa
  • Hukumar JSPCACC Ta Kwato Kudaden Gwamnati Sama Da Naira Miliyan 300
  • Majalisar Dokoki Ta Amince Da Kasafin Kudin 2025 Na Kananan Hukumomin Kaduna 23
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Horas Da Manoman Alkama A Birnin Kudu
  • Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya Ta Kama Wasu Mutane 2 Da Yin Sojan Gona
  • Hajj 2025: NAHCON Ta Rage N54bn Daga Kudaden Cajin Maniyyata
  • NAHCON Ta Rage N54bn Daga Kudaden Cajin Maniyyata, Ta Tsawaita Rajistar Hajjin 2025
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Aikin Gyaran Titin Birnin Kudu Akan Kudi Naira Biliyan 11.5
  • Mataimakin Shugaban APC Da Mambobi 7,500 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Bauchi