HausaTv:
2025-02-26@10:53:40 GMT

An Nada Obasanjo Mai Shiga Tsakani A Rikicin Congo

Published: 26th, February 2025 GMT

An naɗa wasu dattawan Afirka da suka yi mulki a kasashen yankin a matsayin masu shiga tsakani domin warware takaddamar da ta barke a tsakanin ’yan tawayen M23 da gwamnatin Dimokuraɗiyyar Congo.

Kungiyoyin raya kasashen gabashi (EAC) da kudancin nahiyar Afirka (SADC) ne suka naɗa tsoffin shugabannin Habasha da Kenya da Nijeriya domin sanya idanu a kan batun sulhu a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo inda yaki ya kazanta a gabashin ƙasar.

Shugabanin kasashen gabashi da kudanci da ma yammacin Afirka ne suka yi nadin a wani yunƙuri na kawo karshen yaƙin basasa a gabashin Congo, tare da cimma matsaya kan batun yarjejeniyar samar da zaman lafiya a tsakanin ’yan tawaye da gwamnatin Kinshasa ke zargi na samun goyon bayan Rwanda da hukumomi na gwamnatin tsakiya.

Da yammacin jiya Litinin, suka fitar da sanarwar cewa sun nada tsohon shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta da tsohon Firai Ministan Habasha, Hailemariam Desalegn da kuma tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo a matsayin wadanda za su taimaka wajen aiwatar da sabuwar yarjejeniyar sulhu.

“An bukaci dukkan bangarorin su mutunta tsagaita wutar da aka ayyana a taron EAC da SADC, kuma an yi kira ga M23 da kuma sauran bangarorin su dakatar da kutsawa cikin gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo tare da mutunta tsagaita wuta,” in ji kungiyoyin a wata sanarwar da suka fitar.

Har yanzu kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU sun gaza shawo kan rikicin na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongon wanda ya laƙume rayukan fararen hula da dama.

Yaki a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 7,000 a wannan shekarar, kamar yadda Firaiministar kasar Judith Suminwa Tuluka ta shaida wa kwamitin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Xi Ya Tattauna Da Putin Ta Wayar Tarho 

Shugaba Xi ya kuma yi nuni da cewa, a watan Satumban bara, Sin da Brazil, tare da wasu kasashe masu tasowa, sun kafa kungiyar abokan zaman lafiya game da rikicin kasar Ukraine, don samar da sarari da kuma ingantattun sharudda domin karfafa warware rikicin a siyasance. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Nada Tsoffin Shugabannin Najeriya, Kenya, Da Ethiopia Domin Shiga Tsakani A Rikicin Congo
  • An naɗa Obasanjo mai shiga tsakani a rikicin Kongo
  • Mutum 7,000 Suka Mutu A Rikicin Gabashin Kwango Tun Daga Watan Janairu
  • MDD : Kwamitin Sulhu ya amince da kudurin Amurka kan rikicin Rasha da Ukrain
  • Rasha : Putin Ya Ce Turawa ‘Na Iya Shiga’ A Sasanta Rikicin Ukraine
  • Xi Ya Tattauna Da Putin Ta Wayar Tarho 
  • Gwamnatin Iraki Ta Kokawa Sabuwar Gwamnatin Siriya Dangane Da Barazanar Mayakan Daesh Da Suka Rage A Kasar
  • Iran na da niyyar kara karfafa alakarta da kasashen Afirka
  • Kasashen Sin da Afirka ta Kudu sun kara zurfafa alakar da ke tsakanin juna