Iyalan Malcolm X sun nemi Trump da ya yi bayani kan makomar batun kisansa
Published: 26th, February 2025 GMT
Iyalan Malcolm X, bakar fata fata kuma daya daga cikin jagororin musulmin Amurka da aka kashe a ranar 21 ga Fabrairun 1965, sun bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya bayyana bayanan da ke da alaka da kashe shi, kamar yadda shafin Arabi 21 ya ruwaito.
Iyalan Malcolm X sun gabatar da bukatar ne a cikin wata sanarwa da Ben Crump, lauya mai kare hakkin bakar fata a Amurka ya bayar, a wani taro da aka gudanar tare da iyalan Malcolm X a birnin New York na kasar Amurka domin cika shekaru 60 da kashe shi.
Crump, ya yi nuni da wani umarni da Trump ya sanya wa hannu a watan Janairu, inda ya bayyana dukkan bayanan da suka shafi kisan gillar John F. Kennedy, da Martin Luther King, Jr., inda ya bukaci Trump da ya bayyana duk wasu bayanai da suka shafi kisan Malcolm X.
Crump ya bayyana fatansa na cewa Trump zai amsa bukatun iyalan Malcolm X. “Muna sa ran Trump zai dauki mataki a ranar 19 ga Mayu, 2025, a bikin cika shekaru 100 da haihuwar Malcolm X,” in ji shi.
A ranar 19 ga Mayu kowace shekara, Amurkawa da yawa suna bikin “Ranar Malcolm X” don girmama shi a matsayin daya daga cikin fitattun masu fafutukar kare hakkin bakar fata a Amurka a cikin shekarun 1960.
Malcolm X ya kasance kwararre wajen Magana da kaifin basira da kuma kwarjini. Amurkawa da dama sun kadu a lokacin da labarin kisansa ya yadu a shekara 1965.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Tana Shirin Mikawa HKI Dubban Boma-Bomai Cikin Makonni Masu Zuwa
Gwamnatin Amurka ta amince da shirin mikawa HKI dubban boma-bomai saboda kashe falasdinawa a Gaza.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, sojojin HKI suna jiran isowar boma-bomai daga kasar Amurka don fara wani aikin soje na musamman a Gaza. Saboda kawo karshen samuwar Falasdinawa a yankin.
Wata majiyar HKI, yahudawa ta fadawa kamfanin dillancin labaran ‘Ynetnews’ kan cewa sojojin sama na HKI su na dakon isowar boma-bomai har 3000 daga kasar Amurka a cikin yan makonni masu zuwa.
Labarin ya kara da cewa rundunar ta na son ta gudanar da ayyukan soje mai fadin gaske a kan Falasdinwa wanda ya zai kawo karshen Hamas ya kuma kawo karshen samuwar Falasdinawa a yankin.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin kasar Amurka ta na shirin aiko da wani karin boma –bomai har 10,000 nan gaba. Yahuda zasu yi amfani da wadannan boma-boman don fadada ayyukansu a yankin, wadanda suka hada da Siriya da Lebanon da kuma ita Gaza.