HausaTv:
2025-02-26@11:50:31 GMT

Shugaban Iran ya sha alwashin inganta hadin gwiwa da Rasha

Published: 26th, February 2025 GMT

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi alkawarin kara bunkasa huldar Iran da Rasha ta hanyar kara  kaimi wajen ga yarjejeniyoyin da ke tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaba da mu’amala da cudanya mai ma’ana kan harkokin yankin.

A yayin ganawar da ya yi da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da ke ziyara a kasar, Pezeshkian ya bayyana dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da cewa tana kara habaka, tare da jaddada bukatar gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin da ke tsakaninsu, musamman ma cikakkiyar yarjejeniyar hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen biyu.

Ya ce, “Iran da Rasha suna da rawar gani da za su iya takawa domin  inganta hadin gwiwarsu, kuma mun kuduri aniyar karfafa huldar dake tsakanin Tehran da Moscow,” in ji shi.

Ya kuma jaddada muhimmancin ci gaba da yin cudanya mai ma’ana a tsakanin kasashen biyu.

Shugaban ya kara da cewa, “Iran da Rasha suna da ra’ayoyi iri-iri kan batutuwan da suka shafi yankin, kuma suna neman karfafa hadin gwiwarsu a matakai na kasa da kasa, ta hanyar huldar dake tsakaninsu, da kuma kungiyoyi irinsu kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da kungiyar Eurasia, da BRICS.”

Ministan na Rasha ya kuma jaddada cewa, za a yi duk mai yiwuwa don dorewa da kuma kara habaka wannan hadin gwiwa.

Lavrov ya ce, kammala shigar Iran cikin kungiyar tattalin arzikin Eurasia zai samar da wata sabuwar hanya mai inganci don karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu – musamman a fannin tattalin arziki da cinikayya.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: hadin gwiwa

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Ta Mai Da Martani Kan Takardar Bayani a Kan Manufar “Zuba Jari A Amurka Ta Zamanto Farko”

Mai magana da yawun kwamitin sa kaimi ga cinikayya tsakanin Sin da ketare ya amsa tambaya da manema labarai suka gabatar masa kan takardar bayani a kan manufar “Zuba jari a Amurka ta zamanto farko” a gun taron manema labarai da aka gudanar a jiya Lahadi. Inda ya ce, bangaren masana’antu da kasuwancin Sin na matukar kin yarda da matakin da Amurka ta dauka, wanda ya yi gamin-gambiza da batun tsaron kasa wuri guda, sannan ya yi hannu riga kwata-kwata da tsarin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Kakakin ya kara da cewa, Amurka ta tsaurara matakan tsaro da nufin fakewa da guzuma ta harbi karsana a kan shigo da jari daga bangaren Sin a fannin kimiyya da manyan ababen rayuwa da kiwon lafiya da aikin gona da makamashi da kayayyakin da ake sarrafawa da sauransu, a hannu guda kuwa, ta yi yunkurin habaka takaita zuba jarinta a kasar Sin ta hanyar daukar matakan sanya takunkumi da tantance harkar kudade da sauransu. Kuma da zarar an aiwatar da matakan da ake dauka, za su kara tagayyara manufofin da kamfanoni za su aiwatar, zai yi matukar illa ga zaman oda da dokar cinikayyar duniya da haifar da rashin tabbaci ga tsarin samar da kayayyaki a duniya.

Kakakin ya ce, “Sin na kalubalantar Amurka da ta mutunta ka’idar kasuwanci da yin takara daidai wa daida, da kuma fahimtar ainihin iyakar batun tsaron kasar da soke kayyade zuba jari tsakanin kasashen biyu ta yadda za a shimfida yanayi mai yakini ga masana’antu da kasuwancin kasahen biyu kan hadin gwiwarsu ta moriyar juna.” (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Ta Jaddada Kudurin Hadin Gwiwa Da Kasa Da Kasa Kan Hakkin Dan Adam
  • Ministan Harkokin Wajen Rasha Ya Fara Ziyarar Aiki A Nan Tehran
  •  An Yi Ganawa A Tsakanin Ammar Hakim Na Iraki Da Shugaban Kasar Masar Abdufttah Al-Sisi
  • MDD : Kwamitin Sulhu ya amince da kudurin Amurka kan rikicin Rasha da Ukrain
  • Sin Ta Mai Da Martani Kan Takardar Bayani a Kan Manufar “Zuba Jari A Amurka Ta Zamanto Farko”
  • Kar A Ji Tsoron Aikace-Aikacen Kasar Amurka
  • Iran na da niyyar kara karfafa alakarta da kasashen Afirka
  • Kasashen Sin da Afirka ta Kudu sun kara zurfafa alakar da ke tsakanin juna
  • Tawagar Iran a Beirut ta gana da shugabannin Lebanon