Mayaƙan Boko Haram sun sace kwale-kwale 8 a Borno
Published: 26th, February 2025 GMT
Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun yi fashi da makamin wasu kwale-kwalen kamun kifi guda takwas a hannun masunta a Doron Baga da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a ƙauyen Kaimo da ke da tazarar kilomita huɗu daga garin Doron Baga.
A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ‘yan ta’addan dauke da muggan makamai da ba a tabbatar da adadinsu ba, sun mamaye ƙauyen inda suka tara masuntan waje guda.
Majiyar ta ce “sun iso ne da makamai, inda suka yi barazanar tayar da hankali idan ba mu bar jiragen ruwanmu ba.”
Ya ƙara da cewa “daga nan ne ‘yan ta’addan suka ƙwace kwale-kwale guda takwas sannan suka tsere ta cikin kogin.
“Muna buƙatar gwamnati ta kawo mana agaji saboda sana’o’in da muke da su a halin yanzu su ne kamun kifi da noma, amma yanzu muna cikin firgici saboda daji ba shi da tsaro.”
A bayan nan dai rahotannin sun tabbatar da cewa ‘yan ta’addar Boko Haram na ci gaba da kafa sansani a gabar tafkin Chadi, musamman a Tumbun Alkali, Tumbun Barebari, Musarram, Shangaram, da Masharam, duk a cikin Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram jihar Borno Kwale kwale
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Mutane Da Dama A Tsakiyar Najeriya
Wasu masu dauke da makamai sun kai hari a wasu kauyuka biyu dake jihar Filato inda su ka kashe mutane 52.
Rahotannin da suke fitowa daga jihar ta Filato sun ambaci cewa wasu makiyaya ne su ka kai harin na ranar Litinin din da ta gabata an kai shi ne a kan yankin Bassa.
Kamfanin dillancin labarun Reuters da ya dauki labarin ya ambaci cewa,an gano gawawwaki 51 daga cikin wadanda aka kashe din, kuma wani adadi mai yawa na mutanen kauyukan sun jikkata.
Ita kuwa kungiyar “Amnesty International” ta ambaci cewa maharan sun kuma rusa gidaje, tare da wawashe kayan da suke cikinsu. Kungiyar ta zargi jami’an tsaron kasar da gajiyawa wajen tabbatar da tsaro.
Jahar Filato ta dade tana fuskantar fadace-fadace a tsakanin makiyaya da mazauna kauyuka, duk da cewa daga baya an sami lafawar al’amurran,amma daga baya ya sake dawowa.