Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Attahiru Jega, ya yi gargadin cewa tasirin dimokuradiyya a Afirka ta Yamma na raguwa saboda rashin shugabanci nagari. Da yake jawabi a Abuja ranar Talata a matsayin babban mai jawabi a wani taro mai taken, “Mahanga kan makomar zabe a Afirka ta yamma”, wanda wata kungiyar al’umma ta ‘Yiaga Africa’ ta shirya, ya danganta komowar juyin mulkin soji a yankin da rashin shugabanci nagari.

An Gudanar Da Taron Dandalin Ciniki Tsakanin Sin Da Habasha A Addis Ababa Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa Ya yi nuni da juyin mulkin baya-bayan nan da aka yi a Mali, Burkina Faso, Guinea, da Nijar, a matsayin alamu karara na nuna rashin gamsuwa da tsarin mulkin shugabannin yankin, inda ya zarge su da fifita bukatun kashin kai fiye da bukatun ‘yan kasarsu. “Waɗanda ake kira zaɓaɓɓun wakilan jama’a sun mayar da dukiyar jama’a zuwa ga bukatun kashin kansu,” in ji shi. Jega ya yi zargin cewa, koma bayan dimokuradiyya da gazawar gwamnati ke haifarwa ne ya bai wa sojoji damar juyin mulki, wanda ke kawo barazana ga zaman lafiyar yankin. Ya kuma soki shugabannin siyasa da yin magudin zabe domin ci gaba da rike madafun iko maimakon karfafa dimokuradiyya. “Zabuka sun zama wata hanya kawai ta tafka magudi don bai wa shugabannin da ke kan kujerar mulki ci gaba da rike madafun iko,” in ji shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ministan Gidaje, Ba Ɗan Jam’iyyar APC Ba Ne – Shugaban APC Na Kano

Ministan ya yi zargin cewa, furucin Shugaban na daya daga cikin dalilan da suka sa Allah ya karbe mulki daga jam’iyyar duk da nasarar da ta samu a zaben gwamna na 2023.

 

Amma da yake mayar da martani, Abbas ya yi zargin cewa Ata ya yi wa jam’iyyar zagon kasa a zaben 2023, kuma sun bayyana haka ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

 

Abdullahi Abbas ya ce, “A gare mu ‘yan APC Yusuf Ata ba dan jam’iyyar APC ba ne. Ba mu ma san dalilin da ya sa aka nada shi minista ba. Duk fadin jihar Kano a karamar hukumarsa ne muka zo na uku a zaben 2023.

 

“Ba mu san cewa an nada shi minista ba. Mun gaya wa shugaban kasa cewa shi ba dan jam’iyyarmu ba ne. Ya yi wa jam’iyyar zagon kasa.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Zimbabwe Ya Kaddamar Da Yankin Masana’antu Da Sin Ta Zuba Jari
  • Luwaɗi: An yanke wa ɗalibai biyu hukuncin bulala a bainar jama’a
  • Hukumar NPC Za Ta Gudanar Da Kidayar Jama’a Cikin Aminci- Shugaba Tinubu
  • Ministan Gidaje, Ba Ɗan Jam’iyyar APC Ba Ne – Shugaban APC Na Kano
  • Abin da ya sa na yi wa Buhari juyin mulki —Babangida
  • Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje 
  • Yadda jama’a suka kama ɗan shekara 65 ɗauke da bindiga
  • Sheikh Kassim: Gwagwarmaya Za Ta Ci Gaba Da Dukkanin Karfinta
  • Matuƙar Abdullahi Abbas Ya Cigaba Da Zama Shugaban APC A Kano, Zan Fita – Ata