Gwamnati Ta Tabbatarda Kungiyoyin Hadaka A Matsayin Ginshikin Ci gaban Al’umma
Published: 26th, February 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta ce ta gano irin muhimmiyar gudunmuwar da kungiyoyin hadaka ke takawa wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaban al’umma, da kuma karfafa jama’a a kasar.
Karamin Ministan Noma da Tsaron Abinci, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, ya bayyana hakan yayin kaddamar da shirin horo na musamman ga shugabanni, kwamitocin gudanarwa, da manajoji na kungiyoyin hadaka a Najeriya, wanda aka shirya a Kaduna.
A cewar Kungiyar Hadaka ta Duniya (International Cooperative Alliance), sama da kashi 12% na al’ummar duniya suna cikin daya daga cikin kungiyoyin hadaka miliyan 3 a duniya.
Kungiyoyin hadaka suna nada muhimmiyar gudunmuwa wajen bunkasa tattalin arziki mai dorewa, inda suke samar da ayyukan yi da damammaki ga mutane miliyan 280, wanda ya kai kimanin kashi 10% na ma’aikatan duniya.
Kungiyoyin hadaka 300 mafi girma da kamfanonin taimakon juna suna samar da kudaden shiga har dala tiriliyan 2.4, kamar yadda rahoton World Cooperative Monitor na 2023 ya nuna.
A cewar Karamin Ministan Noma da Tsaron Abinci, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, domin cika burin farfado da wannan bangare, Gwamnatin Tarayya ta kuduri aniyar samar da horo da damammakin ci gaban shugabanni da manajoji na kungiyoyin hadaka a jihohi 36 na Tarayya ciki har da Babban Birnin Tarayya (FCT).
Ya ce yayin da gwamnati ke aiwatar da Shirin Sabon Fata don bangaren kungiyoyin hadaka, tana daukar matakan gyara da farfado da tsarin domin mayar da martabar kungiyoyin hadaka a matsayin mai karfi wajen ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a Najeriya.
Dakta Aliyu Sabi Abdullahi ya kuma bayyana cewa gyaran zai mayar da hankali kan dubawa da gyaran dokar Nigeria Cooperative Act don daidaita ta da kyawawan dabi’un duniya da yanayin gida.
Samar da tsari mai kyau na lura da gudanarwar kungiyoyin hadaka don tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Samar da tsare-tsaren sa ido don kawar da kungiyoyin hadaka na bogi da masu zamba.
Ya kuma yaba wa Shugaban Kwalejin Hadaka ta Tarayya Kaduna, Dakta Ibrahim Auwal, bisa kaddamar da wannan shirin horo na musamman da ya yi daidai da tsarin gyara da farfado da bangaren.
A nasa jawabin, Shugaban Kwalejin, Dakta Ibrahim Auwal, ya ce horon zai baiwa mahalarta damar samun kwarewa da ilimin da ake bukata don ci gaban kungiyoyinsu da karfafa al’ummomin da suke wakilta.
Ya jaddada cewa kungiyoyin hadaka su ne ginshikan karfafa tattalin arziki da hade-haden zamantakewa, da ci gaba mai dorewa.
Cov: Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwamnati Gwamnati Ta Tabbatar da Kungiyoyin Hadaka a Matsayin Ginshikin Ci gaban Al umma Matsayin Tabbatarda
এছাড়াও পড়ুন:
Sudan : Janar al-Burhan Ya Shelanta ‘yantar Da Birnin Khartoum
Babban hafsan sojojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya shelanta ‘yantar da Khartoum Babban birnin kasar.
Wannan na zuwa ne bayan da tun da farko ya sanar da cewa dakarunsa sun kwato filin jirgin saman babban birnin, wuri mai matukar mahimmanci daga hannun dakarun ‘yan tawaye na RSF.
“An ‘yantar da Khartoum, an gama,” in ji shugaban na Sudan daga fadar shugaban kasa a wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin na kasar.
Kazalika, wata sanarwa da sashen watsa labarai na majalisar rikon kwarya mai mulkin kasar ta fitar, ta ce Al-Burhan ya sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa dake birnin Khartoum ta jirgi mai saukar ungulu a jiyan, jirgin da ya zamo na farko da ya sauka a filin, tun bayan barkewar tashin hankali a watan Afrilun shekarar 2023.
Daga nan ne kuma ya duba sassan rundunar sojin gwamnati dake tsaron filin jirgin kafin ya wuce zuwa fadar gwamnati.
Tun daga farkon shekarar 2024, dakarun sojin gwamnati na SAF ke ta kwace sassan kasar daban daban, musamman a birnin Omdurman na arewacin Khartoum, inda suka kwace kaso mai yawa na birnin, lamarin da ya karfafa ikonsu sama da na dakarun RSF a yankin.
A ranar Juma’a data gabata, sojojin na sudan sun ayyana kwace iko da fadar gwamnati, da wasu muhimman ofisoshin gwamnatin kasar dake Khartoum, wuraren da a baya suka kasance muhimman sassa da dakarun RSF ke rike da su a birnin na Khartoum.