Aminiya:
2025-03-28@18:45:23 GMT

Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio

Published: 26th, February 2025 GMT

Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da ƙara a kotu tana ƙalubalantar shugaban majalisar, Godswil Akpabio, kan zargin ɓata mata suna.

Natasha ta shigar da ƙarar ne gaban Babbar Kotun Tarayya a ranar Talata, tana mai ƙarar Akpabio da babban mai taimaka masa Mfon Patrick.

Mutum 10 sun mutu a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri Babu hannun Naira Marley a mutuwar Mohbad — Kotu

Ta nemi Kotun Tarayyar da ta umarci waɗanda ake karar su biya ta diyyar naira biliyan 100 kan zargin ɓata mata suna, sannan a biya ta naira miliyan 300 a matsayin kuɗin shigar da ƙara.

Akpoti, wadda lauyanta Victor Giwa ya shigar da ƙarar a madadinta, ya yi ƙorafi kan kalaman da babban mai taimaka wa Shugaban Majalisar Dattawan ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ta nemi kotun ta tilasta wa mutanen janye kalaman, sannan su nemi afuwarta a wani shafin jarida.

Ta ɗora zargin nata ne kan wani saƙo da ta ce Mista Patrick ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya soke ta cewa “ba ta san komai ba game da zaman majalisa…da kuma saka tufafi masu shara-shara.”

Barista Giwa ya yi zargin cewar kalaman ba komai ba ne illa, ɓata suna, da takalar faɗa, da ƙanskantar da ita a idon abokan aikinta, da sauran al’umma.

Sanata Natasha ta buƙaci kotun da ta haramta wa waɗanda ake ƙara ko makusantansa daga wallafa duk wani rubutu na ɓatanci a game da ita.

A makon da ya gabata ne Sanata Natasha Akpoti Uduaghan ta bayyana damuwa kan yadda aka bai wa wani ɗan majalisa wurin zamanta, saboda wasu sauye-sauye da aka yi a tsarin zaman majalisar.

Sanatar ta ƙi amincewa da sauyin wajen zaman da aka yi mata, wanda hakan ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ta da Akpabio.

Lamarin na zuwa ne yayin da aka umarci kwamitin ladabtarwa na Majalisar Dattawan da ya gayyaci Sanata Natasha don bin bahasi kan rikicin sauyin wajen zaman.

A bayan nan ne aka yi zazzafar musayar yawu tsakanin Sanata Natasha da Akpabio kan sauya mata wurin zaman da ta ce an yi ba tare da amincewarta ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: diyya

এছাড়াও পড়ুন:

Mahukuntan Lai Ching-te Sun Salwantar Da Muradun Kasa Wajen Neman ’Yancin Kai Bisa Dogaro Da ’Yan Katsalandan Na Ketare

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu zai sake zama shugaban ƙasa a 2027 — Akpabio
  • Gobara Ta Ƙone Sabon Ginin Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Mata Na Jami’ar Sokoto 
  • Sallah: Yadda ake shirin caɓa ado duk da tsadar kaya
  •  Kasashen Iran Da Katar Sun Jaddada Muhimmancin Shigar Da Dukkanin Bangarorin  Al’ummar Kasar A Cikin  Sha’anin Kasar
  • Wani abu kan Zakkatul Fidir da Sallar Idi
  • Sudan ta Kudu : Ana tsare da Riek Machar a wani gida
  • Mahukuntan Lai Ching-te Sun Salwantar Da Muradun Kasa Wajen Neman ’Yancin Kai Bisa Dogaro Da ’Yan Katsalandan Na Ketare
  • Majalisa Ta Yi Watsi Da Kara Akan Akpabio Kan Zargin Neman Yin Lalata Da Natasha
  • Gwamnatin Kano za ta hukunta masu shigar banza a bikin Sallah
  • Sin Ta Samu Bunkasa A Fannin Neman Ikon Mallakar Fasaha A Ofishin EPO