Amurka : Kungiyar DAWN Ta Bukaci ICC Ta Binciki Biden Kan Laifin Hada Kai Da Isra’ila A Laifukan Gaza
Published: 26th, February 2025 GMT
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta DAWN mai hedkwata a birnin Washington ta yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC da ta binciki rawar da tsohon shugaban Amurka Joe Biden da wasu jami’an Amurka suka taka wajen taimakawa Isra’ila ta aikata laifukan yaki a Gaza.
A bukatar da aka mika wa mai gabatar da kara na kotun ICC Karim Khan a ranar 19 ga watan Janairu, 2025, wacce ta bayyana a ranar Litinin, kungiyar mai zaman kanta ta Democracy Now for the Arab World (DAWN) ta zargi Biden, sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, da sakatarensa na tsaro, Lloyd Austin, da taimakawa Isra’ila ta aikata laifukan yaki a Gaza.
A cewar kungiyar mai zaman kan ta, ana kuma zarginsu da bada gudummuwarsu da gangan wajen aikata wadannan laifuka.
Takardar ta nuna goyon bayan gwamnatin Biden na soja, siyasa ga laifukan Isra’ila, wadanda suka hada da jigilar makamai da suka kai dala biliyan 17.9 tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, musayar bayanan sirri da kariyar diflomasiyya, kamar kin amincewa da kudurin tsagaita wuta da yawa a Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Tsaro.
“Akwai kwararan dalilai na bincikar Joe Biden, Antony Blinken da Lloyd Austin saboda hadin kai a cikin laifukan Isra’ila,” in ji mamban kwamitin DAWN Reed Brody a cikin wata sanarwa, yana mai cewa: “Bama-baman da aka jefa kan asibitocin Falasdinu, makarantu da gidajensu, na Amurka ne, kuma an gudanar da yakin da kisa da zalunci tare da taimakon Amurka. »
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kaduna Ta Jadadda Kudurin Ta Wajen Samarda Tsaftatacen Ruwan Sha Ga Al’umma
Ma’aikatar Ayyuka da Samar da Kayayyakin More Rayuwa, tare da hadin gwiwar First Impression Communication Limited, ta shirya wani taro kan shirin Samar da Ruwa Mai Tsafta a Birane da Karkara da Tsabtace Muhalli da Kiwon Lafiya (SURWASH) da ya gudana a Arewa House, a Kaduna.
Da yake bude taron, Kwamishinan Ayyuka da Samar da Kayayyakin More Rayuwa, Dakta Ibrahim Hamza, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na magance matsalar karancin ruwa a jihar.
Kwamshinan wanda Mataimakin Daraktan Albarkatun Ruwa, David Roven Aliyu ya wakilta, ya bayyana kokarin da gwamnati ke yi, ciki har da gina rijiyoyin burtsatse a wasu al’ummomi domin inganta tsaftar muhalli da kiwon lafiya.
“Shirin SURWASH na Najeriya wani shiri ne da Asusun Bada Lamuni na Duniya (World Bank) ke daukar nauyinsa da dala miliyan 700 domin inganta ayyukan WASH a jihohi bakwai na Najeriya, ciki har da Kaduna.
Manufar shirin ita ce samar da ruwan sha mai tsafta ga mutane miliyan shida da kuma inganta tsaftar muhalli ga mutane miliyan 1.4.
Dakta Hamza ya bayyana cewa an ware kananan hukumomi guda shida a Jihar Kaduna wanda suka hada da —Soba, Igabi, Chikun, Jaba, Jema’a, da Sabon Gari—domin tabbatar da su sun samu tsaftatacen Ruwa Sha a yankunan su.
“Da zarar wadannan yankuna sun cika ka’idojin da ake bukata, za a kara zabar karin kananan hukumomi guda bakwai domin shirin,” in ji shi.
Ya bukaci jama’a su kare kayayyakin tsafta da kiwon lafiya da gwamnati ta samar domin su dade ana amfana da su.
A nasa jawabin, Shugaban Shirin SURWASH na Kaduna, Mista Esau Ambinjah, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar al’umma wajen kare rijiyoyin burtsatse da sauran kayayyakin tsafta.
Ya kuma bayyana cewa an riga an zabi kananan hukumomi guda bakwai—Sanga, Makarfi, Kudan, Zaria, Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu, da Zangon Kataf—domin shirin SURWASH.
A nata jawabin, Shugabar Kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN), Amira Hafsatu Musa Isa, ta bada shawarar cewa ya kamata a sanya abun da ya dace da al’adu da addini a cikin shirye-shiryen wayar da kai.
Haka kuma, Shugabar Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen mata a Kaduna, Bishop Eister Yawai, ta bukaci a fadada yakin wayar da kan SURWASH zuwa wuraren addinai.
Ta bayyana cewa samun tsaftataccen ruwa yana da matukar muhimmanci wajen hana yaduwar cututtukan da ke da nasaba da ruwa.
Ta kuma bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su kara kaimi wajen magance matsalar karancin ruwa a wasu al’umomi.
Wanda ya gabatar da shirin, Yusuf Idris, ya gabatar da sanarwar wayar da kai na SURWASH da aka fassara cikin Hausa da turanci, inda mahalarta suka gabatar da ra’ayoyinsu domin inganta shirin.
Cov/Adamu Yusuf