Shugabannin Afirka Ta Kudu, Malaysia Da Colombia Sun Yi Kira Da A Kawo Karshen Laifukan Isra’ila
Published: 26th, February 2025 GMT
Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malesiya da kuma Colombia sun bukaci da a hukunta laifukan da Isra’ila ke yi na keta dokokin kasa da kasa.
A makalar da suka rubuta a mujalar harkokin waje, shugabannin sun bayyana cewa “Zabin abu ne mai wuyar gaske: ko dai mu yi aiki tare don tilasta dokokin kasa da kasa ko kuma mu yi kasadar rugujewar sa.
Shugabannin sun kara da cewa “harin da ake kaiwa al’ummar Falasdinu ya yi daidai da ababe marasa dadi da munin tarihin da suka faru a cen baya kan kasashensu”, da suka hada da mulkin mallaka, yaki da ta’addanci da wariyar launin fata.
“Muna iya fitowa daga nahiyoyi daban-daban, amma muna da tabbacin cewa rashin tsawatarwa na da hannu cikin irin wadannan laifuka.
Kasashen uku dai dukansu na daga cikin wadanda suka yi tir da Allah wadai da kisan kare dangin da Isra’ila ke aikatawa a zirin Gaza.
Afirka ta Kudu kuma ita ce ta jagoranci shigar da karar Isra’ila a Kotun Duniya ta ICJ, kan laifukan yaki a Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Tsaron Iran Ya Bayyana Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya A Matsayar Alamar Yan Ta’adda
Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta zama babbar alamar ta’addanci a duniya
Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummomin Falastinu da na Lebanon a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa da tarurrukan kasa da kasa suka yi shiru, yana mai cewa: A yau al’ummar yahudawan sahayoniyya ta zama wata babbar alama ta ta’addancin kasa a duniya.
Birgediya Janar Nasirzadeh ya furta haka ne a ganawarsa da ministan tsaron Jamhuriyar Zimbabwe Uba Muchinguri Kashiri a lokacin ziyararsa a kasar Iran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu. A cikin wannan ganawar, ministan tsaron na Iran ya jaddada cewa: Dangantakar dake tsakanin Iran da Zimbabwe tana da tushe mai tarihi, kuma ta kasance a ko da yaushe bisa abota da mutunta juna. Ya kara da cewa, a cikin shekarun da suka gabata, kasashen biyu sun sami ci gaba mai kyau a dangantakar dake tsakanin kasashensu.