Araghchi : Iran Ba Za Ta Shiga Tattaunawa Da Amurka Bisa Matsin Lamba
Published: 26th, February 2025 GMT
Iran ta bayyana cewa ba zata shiga wata tattaunawa da Amurka ba kan shirinta na nukiliya bisa matsin lamba.
Ministan harkokin wajen Iran ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan, inda yake cewa muddin fadar White House ba ta janye matsin lamba wa kasar ba, babu wata tattaunawa.
“A kan tattaunawar nukiliya, matsayin Iran a bayyane yake: ba za mu yi shawarwari cikin matsin lamba, barazana, da takunkumi ba.
“Saboda haka,” in ji ministan harkokin wajen Iran, “babu yuwuwar yin shawarwari kai tsaye tsakaninmu da Amurka kan batun nukiliya matukar dai ana ci gaba da yin amfani da mafi girman matsin lamba a yadda take a halin yanzu.”
Misra Araghchi ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na Rasha, Sergey Lavrov da ke ziyara a Tehran.
Ministan harkokin wajen kasar ya ce Iran za ta magance batun nukiliyar tare da hadin gwiwa da kawayenta – Rasha da China.
A nasa bangare da yake bayyani game da shirin nukiliyar Iran, Lavrov ya ba da fifiko kan hanyar diflomasiyya.
“Mun yi imanin cewa har yanzu akwai karfin diplomasiyya don warware batun nukiliyar Iran, kuma muna fatan za a iya samun mafita. Ba Iran ce ta haifar da wannan rikicin ba.” Inji shi.
Iran dai ta dade tana fuskantar takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata kan ayyukanta na nukiliya, da batun kare hakkin bil’adama, da dai sauransu, saidai zuwan Donald Trump, ya kara dagula al’amuran inda ya sha alwashin matsin lamba kan kasar ta Iran, domin ta mika wuya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Taron Kasa da Kasa Don Tallafawa Yan Gudun Hijirar A Sudan
Jami’an diblomasiyya daga kasashen duniya da dama, da kuma wakilan kungiyoyin agaji daban-daban sun hadu a birnin London na kasar Burtania don tattauna batun yakin da ke faruwa a kasar Sudan wanda a halin yanzu yake cika shekaru 2 ke nan.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Afrika New” ya bayyana cewa, taron na kwana guda ya tattara wakilai daga kasashen Faransa, Burtaniya, Jamus da kuma kungiyar tarayyar Turai, har’ila yau da kasashen da suke makobtaka da kasar ta Sudan.
Labarin ya kara da cewa, yakin na Sudan wanda yake cika shekaru biyu, ya zuwa yanzu ya lakume rayukan mutane akalla 20,000, sannan ya yi sanadiyar kauracewar mutane kimani miliyon 14 zuwa cikin kasar da kuma kasashe makobta, sannan wasu da dama ji raunuka.
Ministan harkokin wajen kasar Burtania David Lammy, a jawabin da ya gabatar a taron na ranar Talaya ya bayyana cewa za’a dauki lokaci kafin a dawo da zaman lafiya a kasar ta sudan, Amma abunda wannan taron yake nema shi ne samun wata kafa ta isar da kayakan agaji ga wadanda suke tsananin bukatarsu a yankuna daban daban na kasar da kasashe makobta.