A yayin da jam’iyyar APC mai mulki ta shirya taron kwamitin zartaswa na kasa wanda ake sa ran za ta yi ranar Laraba, jam’iyyar ta musanta rade-radin da ake yi na cewa shugaba Bola Tinubu na iya neman shugaban jam’iyyar, Dakta Abdullahi Ganduje, ya sauka daga mukaminsa. Sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Ajibola Basiru, ya karyata jita-jitar a wata hira da aka yi da shi, inda ya jaddada cewa, jam’iyyar ta saba gudanar da irin wannan taron, ba wai sai don shirin zabe ba.

Amurka Za Ta Illata Kanta Bisa Tsara Matakan Kayyade Samar Wa Sin Sassan Na’urorin Laturoni Na Semiconductor Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa A halin da ake ciki, tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon ministan birnin tarayya, Nasir El-Rufai, ya tabbatar da cewa ba zai halarci taron jam’iyyar na kasa ba a yayin da yake magana a shirin ‘PrimeTime’ na Arise Television a daren ranar Litinin, inda ya bayyana rashin sanar da shi a matsayin dalilin rashin halartarsa. “Ba zan samu halartar taron kolin jam’iyyar APC na kasa ba. Zan koma birnin Alkahira, inda nake shafe yawancin lokaci na. Ban sami isasshiyar sanarwa ba. Kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu ya bayar da kwanaki 21, ko kuma kwanaki 14 don samun sanarwar gudanar da irin wannan taron. Ba na tsammanin an turo min da gayyatar,” in ji shi. Ya ci gaba da bayyana cewa, “Idan ya kasance, ban samu gayyatar makonni biyu zuwa makonni uku da suka gabata ba. Don haka, ina da tsare-tsare na, kuma gobe zan tafi. Amma abokaina da yawa za su halarta, don haka ba zan rasa kome ba. Zan san abin da aka tattauna.” Babban taron dai, zai kasance karkashin jagorancin shugaba Tinubu, inda ake sa ran mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari za su halarta. Haka kuma akwai shugaban majalisar dattawa Dr. Godswill Akpabio, gwamnonin jam’iyyar APC na baya da na yanzu, tsoffin shugabannin majalisar wakilai da masu rike da madafun iko, shugabannin jam’iyyar na jihohi, kwamitin ayyuka na kasa, da sauran masu ruwa da tsaki.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: jam iyyar APC

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar NPC Za Ta Gudanar Da Kidayar Jama’a Cikin Aminci- Shugaba Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ta dauki wani muhimmin mataki na gudanar da kidayar jama’a da gidaje da aka jima ba a yi ba, inda  ya tabbatar da cewa za a gudanar da aikin cikin inganci ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Shugaban ya ba da wannan tabbacin ne a wata ganawa da ya yi da jami’an hukumar kula da yawan jama’a ta kasa (NPC) a fadar gwamnati, shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin kidayar jama’a ga tsare-tsare na kasa, tare da jaddada aniyarsa na tabbatar da tattara bayanai masu inganci.

Shugaba Tinubu ya bayyana shirin kafa kwamitin da zai duba kasafin kidayar jama’a da kuma gano hanyoyin samun kudade.

Ya kuma jaddada bukatar hukumar kula da tantance ‘yan kasa (NIMC) ta taka rawar gani wajen gudanar da wannan aiki, tare da tabbatar da samar da ingantattun na’urorin tantancewa da suka hada da tantance fuska da murya.

Shugaban ya bayyana cewa ingantattun bayanan  za su haɓaka shirye-shiryen gwamnati, musamman a fannin aikin gona da walwalar jama’a.

Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya tabbatar da kudurin na Tinubu, inda ya bayyana cewa rashin kudi ne ya janyo tsaikon kidayar jama’a.

Ya kuma bayyana cewa, NPC ta riga ta kammala muhimman ayyukan shirye-shirye da suka hada da kidayar jama’a, sannan kuma hukumomin tantancewa da kididdiga daban-daban kamar su NPC, NIMC, NBS, da Ma’aikatar Tattalin Arziki, suna  aiki tare don inganta bayanan da ake da su.

 

Daga Bello Wakili

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Buhari da El-Rufai ba su halarci babban taron APC ba
  • Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa
  • Shugabannin Afirka Ta Kudu, Malaysia Da Colombia Sun Yi Kira Da A Kawo Karshen Laifukan Isra’ila
  • IRGC : Jana’izar Nasrallah Wani Sakon ‘yan Gwagwarmaya A Duniya Baki Daya
  • Hukumar NPC Za Ta Gudanar Da Kidayar Jama’a Cikin Aminci- Shugaba Tinubu
  • IRGC Ta Bayyana Cewa Taron Jana’izar Nasarallah Ya Yi Tisara A Duniya Gaba Daya Saboda Barazanar Da Jiragen Yakin HKI Ta Yi Wa taron
  • Ministan Gidaje, Ba Ɗan Jam’iyyar APC Ba Ne – Shugaban APC Na Kano
  • Abin da ya sa na yi wa Buhari juyin mulki —Babangida
  • Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyararsa A Birtaniya Da Ireland Da Halartar Taron Kolin Kwamitin Sulhu Da Na Tsaro A Munich Da Na G20