HausaTv:
2025-02-26@15:49:33 GMT

                          Me Turkiya Take So A Syria?

Published: 26th, February 2025 GMT

 A farko-farkon da masu dauke da makamai su ka kwace iko da birnin Halab, jami’an gwganatin Turkiya sun kaucewa yin Magana akan abinda yake faruwa.

Sa dai kuma da yake mai kaza a aljihu ba ya jimirin cas, ba a je ko’ina ba, su ka fara furta kalaman da suke nuni da cewa, Da kawai rina a kaba. Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Fidan, ya yi tsokaci akan abinda yake faruwa a Syria, ya zargi  tsohuwar gwamnatin Syria da cewa; Ba ta yi aiki da bangarorin yarjejeniyar Astana ba.

Sojojin Turkiya suna cikinm kasar Syria tun a farkon 2018, inda suke mamaye da kaso 10% na yankin wannan kasa. Kuma aiki a tare da masu adawa da gwamnatin Damascuss,musamman rundunar da ake kira da             “ Sojojin Kasar Syria” wacce aka kafa  a cikin garin Orfa a ranar 4 ga watan Oktoba na shekarar 2019. Kafa wannan rundunar ya kasance kwanaki kadan gabanin hasken da Amurka da Rasha su ka bai wa Turkiyan ta kai wa Kurdawa hari a gabashin tekun Euphrates.

 Turkiya din ce take bai wa wannan runudnar makami da kudi da albashi da dukkanin abinda suke bukata domin maye gurbin rundunar “ Free Syrian Army” wacce ita ma a cikin kasar Turkiya aka kafa ta a  watan Ogusta na 2011.

 Kafafen watsa labarun Turkiya suna kaucewa ambaton rawar da gwamnatin kasar tasu take takawa a cikin abubuwan da suke faruwa a cikin Syria. Abinda suke cewa shi ne: “ Rundunar ‘yan adawa ta Syria”, ko kuma su kira su da “ Masu adawa da Assad.” Haka nan kuma suna kiransu da |Rundunar Hatsh” ba tare da sun fayyace abinda wadannan haruffan  hudu suke nufi ba da kuma alakarta da rundunar; Jubhatun-Nusrah’. Wannan kungiyar kuwa sunanta ta ‘yan ta’adda a bisa dokar da shugaban Turkiya Urdugan ya rattabawa hannu a ranar 29 ga watan Ogusta na 2018.

Kafafen watsa labarun gwamnati na Turkiya ba su Magana akan alakar da take a tsakanin rundunar  Jaisuhl Watani al-Suri”da kuma |Hay’atult-tahirish-sham.” da suke a cikin garin Idlib, kuma Turkiyan ce ta rika ba su dukkanin abubuwan da suke bukatuwa da su na man fetur, wutar lantarki, ruwa, internet, da dukkanin hajar da ake amfani da ita ta yau da kullum. Tsakanin iyakar Turkiya zuwa Idlib, kilo  mita 40 ne kadai.Bugu da kari ana kashe kudaden Turkiya a cikin wannan yankin na Idlib. Haka nan kuma babu wata hanyar da za iya shiga cikinsa sai ta hanyar Turkiya, wato dai a fakaice za a iya cewa, an yanke wanann yankin da Syria ya zama wani bangare na Turkiya.

Bayan wannan, kafafen watsa labarun na Turkiya sun rika Magana akan muhimmancin  da garin Halab yake da shi a wurin Turkiya, ko da kuwa na wucin gadi ne. Hakan ta faru ne bayan da rundunar “Jaishul Watani al-Suri” ya kwace iko da garin Tal-Rif’ da kuma korar  mayakan Kurdawa daga cikinsa, haka nan wasu unguwanni a cikin birnin na Halab.

Kurduwan dai sun shimfida ikonsu ne a cikin wadannan yankunan bisa yarjejeniya da  tsohuwar gwamnatin Damascuss.

Kafafen watsa labarun na Turkiya sun rika bayyana abinda ya faru da cewa, bugu ne mai kyau da aka yi wa Kurdawa da kawo musu cikas, a kokarin da suke yin a kafa yankinsu mai cin gashin kansa a cikin Syria. Haka nan kuma kafafen watsa labarun ta Turkiya sun rika yi wa Kurdawan barazana cewa sojoji za su mamaye gabashin tekun “Eupherate” da can ne cibiyar kurdawan idan an gama da ‘yantar da dukkanin Syria da kifar da gwamnatin Asad.

 Bugu da kari, kafafen watsa labarun Turkiyan sun rufe idanunsu akan yadda  daruruwan masu dauke da makamai da su ka shiga cikin birnin Halab, suke Magana da harshen turkanci da Karin harshe irin an Uzabakistan, Shishan, da Kuma Egoz na kasar China.

 **

Wani abu da ya fi bayar da mamaki shi ne yadda wasu Turkawa, su ka fara cewa, ai dama gundumar Halab, ta turkiya ce, domin tana a karkashin Daular Usmaniyya har zuwa 1918, an kuma kori Turkawa daga ciki ne bayan da aka yi galaba akan Daular Usmaniyya a yakin duniya na farko.

Wannan labarin na Turkiya, ya yi kama da abinda Turkawan su ka rika fada a lokacin abinda aka kira da “Yunkurin Larabawa” a 2011 da su ka rika yin bore a cikin kasashe mabanbanta domin samun ‘yanci. A wancan lokacin Turkawan sun rika cewa, yankunan Halab, Idlib, Riqqah, Deir-zur, da kuma arewacin Iraki wato Mausel,  Karkuk da Arbil da Sulaimaniyya, duk wani yanki ne na Turkiya. Wasu kuma sun rika cewa, Idlib ce jahar Turkiya ta 81.

 Bugu da kari an rika ganin hotuna da tutocin Turkiya akan ginin “Wani tsohon gini mai tarihi na garin Halab.

A ranar Talata 10 /12/2024 shugaban kungiyar kishin turkancin “Daulat Bahshali “ya bayyana cewa” Halab Gari ne na Turkawa.”

Loakcin da ‘yan tawayen masu dauke da makamai suke shirin shiga garin Halab, Turkiya ta umarce su da kar su cutar da mazaunasa domin ba ta damar aiwatar da shirinta na tattalin arziki wanda ya kunshi, ba su wutar lantarki, man fetur da dukkanin hajojin da suke da bukatuwa da su. Wanann shi ne abinda Turkiyan ta tsara a tsawon shekaru 13 na yaki.

Ankara ta so ganin cewa duk inda  ‘yan tawaye su ka shiga su yi kyakkyawar mu’amala da mutane, saboda ita kuma ta ci moriyar hakan ta fuskar tattalin ariziki.

A karshe kuwa, mayakan sun shiga birnin Damscuss, inda su ka zama gwaraza, sannan kuma Turkiya ta zama wata gwarzuwa da kuma a nan gaba za ta ci moriyar taimakawa ‘yan adawa na shekaru masu tsawo, ta fuskokin siyasa da tattalin arziki.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar NPC Za Ta Gudanar Da Kidayar Jama’a Cikin Aminci- Shugaba Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ta dauki wani muhimmin mataki na gudanar da kidayar jama’a da gidaje da aka jima ba a yi ba, inda  ya tabbatar da cewa za a gudanar da aikin cikin inganci ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Shugaban ya ba da wannan tabbacin ne a wata ganawa da ya yi da jami’an hukumar kula da yawan jama’a ta kasa (NPC) a fadar gwamnati, shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin kidayar jama’a ga tsare-tsare na kasa, tare da jaddada aniyarsa na tabbatar da tattara bayanai masu inganci.

Shugaba Tinubu ya bayyana shirin kafa kwamitin da zai duba kasafin kidayar jama’a da kuma gano hanyoyin samun kudade.

Ya kuma jaddada bukatar hukumar kula da tantance ‘yan kasa (NIMC) ta taka rawar gani wajen gudanar da wannan aiki, tare da tabbatar da samar da ingantattun na’urorin tantancewa da suka hada da tantance fuska da murya.

Shugaban ya bayyana cewa ingantattun bayanan  za su haɓaka shirye-shiryen gwamnati, musamman a fannin aikin gona da walwalar jama’a.

Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya tabbatar da kudurin na Tinubu, inda ya bayyana cewa rashin kudi ne ya janyo tsaikon kidayar jama’a.

Ya kuma bayyana cewa, NPC ta riga ta kammala muhimman ayyukan shirye-shirye da suka hada da kidayar jama’a, sannan kuma hukumomin tantancewa da kididdiga daban-daban kamar su NPC, NIMC, NBS, da Ma’aikatar Tattalin Arziki, suna  aiki tare don inganta bayanan da ake da su.

 

Daga Bello Wakili

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugabannin Afirka Ta Kudu, Malaysia Da Colombia Sun Yi Kira Da A Kawo Karshen Laifukan Isra’ila
  • Isra’ila Ta Kai Hare-hare A Kudancin Syria
  • Hamas ta yi tir da matakin Isra’ila na shirin takura masu ibada a masallacin Quds
  • Nebenzia : Hare-haren Sojojin Isra’ila a Lebanon da Syria na kara dagula lamura a yankin
  • Manoman tumatir na tafka asara saboda faɗuwar farashi
  • Araghchi : Bai Kamata A Rika Murgude Hakkin Dan Adam Ana Shishigi A Harkokin Cikin Gidan Kasashe Ba
  • Hukumar NPC Za Ta Gudanar Da Kidayar Jama’a Cikin Aminci- Shugaba Tinubu
  • Iran A Karon Farko Ta Gwada Aiki Da Sabbin Jiragen Yakin Da Ta Kera A Cikin Atisayen Zulfikar da Ke Gudana A Halin Yanzu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Al’umma Da Su Rika Taimakawa Hukumomin Tsaro Da Muhimman Bayanai