Gwamnatin Jigawa Za Ta Biya Diyar Sama Da Naira Biliyan 5 Ga Wadanda Aikin Tituna Ya Shafa
Published: 26th, February 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan Biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin gari ya shafa.
Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse.
A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na yanki suka gabatar.
Ya ce, majalisar ta kuma amince da kashe sama da naira biliyan takwas da miliyan dari biyu a matsayin kashi 30 bisa na kudaden shirin noman rani na shinkafa na shekarar 2025.
Ya kuma yi bayanin cewa, an amince da hakan ne da nufin samar da wadataccen abinci da inganta rayuwar miliyoyin al’ummar Jigawa ta hanyar bai wa Manoma 58,500 rance, don noma hekta 50,000 na shinkafa a fadin yankunan da ake noman shinkafa, kamar yadda ma’aikatar noma da albarkatun kasa ta gabatar.
Kwamishinan ya ce, majalisar zartaswa ta jihar ta kuma amince da sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita wa’adin shekaru 2 tsakanin ma’aikatar lafiya ta gwamnatin jihar Jigawa da kungiya mai zaman kanta ta Medicins San Frontiers (MSF) da ke kasar Faransa.
A cewarsa, rattaba hannu kan yarjejeniyar na da nufin karfafa kokarin jihar na rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, ta hanyar samar da ingantacciyar kula ga masu juna biyu a babban asibitin Jahun da kuma cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na Miga da Ajura.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Alhazai Ta Jihar Kano Ta Tsawaita Wa’adin Biyan Kudin Aikin Hajji
Biyo bayan umarnin da hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta bayar, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta kara wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025.
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a yau yayin taron bita ga ma’aikata da jami’an Alhazai na kananan hukumomi a Otal din Grand Central.
Alhaji Danbappa ya bayyana cewa za a ci gaba da karbar kudaden maniyyata har zuwa ranar daya ga watan Ramadan.
Ya kuma bayyana cewa, ya zuwa yau 25 ga watan Fabrairun 2025, hukumar ta bada sama da naira biliyan 22 ga hukumar alhazai ta kasa a madadin Alhazan jihar Kano.
Bugu da kari, babban daraktan ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa gaugawar daukar mataki na magance bukatun hukumar a duk lokacin da ake bukata.
A nasa jawabin shugaban hukumar gudanarwar Alhaji Yusif Lawan ya bukaci ma’aikata da jami’an Alhazai na kananan hukumomi da su kara himma wajen gudanar da ayyukansu.
Abdullahi Jalaluddeen