Aminiya:
2025-04-18@09:39:07 GMT

Ƙungiya ta raba wa marayu da mabuƙa kayan makaranta a Kano

Published: 26th, February 2025 GMT

Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta.

Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi.

Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino

Sakataren ƙungiyar, Kwamared Usman Bello Kofar Mata, ya ce sun bayar da taimakon ne, domin rage yawan yara da ke gararamba a tituna, musamman marayu.

“Mun ga yadda wasu yara ke shiga tsaka mai wuya bayan rasuwar iyayensu.

“Wasu ba su da kowa da zai kula da su, sai dai su riƙa yawo kamar awaki. Don haka, muka yi bincike muka zaƙulo irin waɗannan yara don mu taimaka musu,” in ji shi.

Taron rabon kayayyakin ya samu halartar mai unguwar Kofar Mata, Alhaji Muhammad Jibril, wanda ya yi kira da a riƙa taimakon marayu da mabuƙata domin hana lalacewar tarbiyyar yara a yankin.

Ya ce rashin irin wannan taimako ne ke janyo koma-baya a yankin Arewa, inda ya bayar da misali da Kudancin Najeriya inda ake ɗaukar nauyin marayu har su girma su zama mutane nagari a rayuwa.

“Idan har ba a taimaka wa marayu da mabuƙata ba, za su tashi babu tarbiyya.

“Idan yaro ba shi da gata, babu wanda zai gyara masa hanya. Amma idan ana tallafa masa, zai girma da sanin darajar rayuwa,” in ji shi.

Ya buƙaci iyaye da al’umma su ci gaba da kula da tarbiyyar yara tare da basu kulawa da taimako domin su zama mutane nagari da za su amfanar da al’umma.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kayayyakin Makaranta Kofar Mata Ƙungiya Marayu

এছাড়াও পড়ুন:

Matan da suka tsira daga Boko Haram na buƙatar tallafin musamman

Mata da ’yan mata da suka tsira daga tashin hankalin ‘yan Boko Haram a Arewa Maso Gabashin Nijeriya na fuskantar matsaloli masu yawa, ciki har da shiga tsananin damuwa da fuskantar nuna wariya da rashin samun dama na neman kuɗi da kuma uwa-uba rashin samun kulawar gwamnati da na al’umma.

A lokacin tashin hankali da yaƙe-yaƙe mata da yara ne suka fi shan wahala sosai daga munanan hare-haren da ke shafar lafiyar jikinsu da ta ƙwaƙwalwarsu, sannan sun fi kowa faɗawa matsalar tattalin arziƙi da shiga cikin ɗimuwa.

Gwamnatin Yobe ta sayo hatsi don tunkarar kakar bana ’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista

Tun farkon fara rikicin Boko Haram a watan Yulin 2009, mata da yara a Arewa Maso Gabas sun kasance cikin waɗanda aka aka fi ci wa zarafi. Yawancinsu a kan tilasta musu shiga yaƙi inda ake amfani da su a matsayin ‘yan ƙunar baƙin wake, ko a yi amfani da su a matsayin garkuwa.

Da yawansu sun rasa rayukansu, wasu an ci zarafinsu ta hanyar fyaɗe, sannan kuma an hana su damar ci gaba da neman ilimi. Har ila yau, an sace ɗaruruwansu kuma aka yi amfani da su tamkar bayi.

Fiye da mata miliyan biyu da ƙanana yara sun rasa matsugunansu, inda aka tilasta musu tserewa zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira ko wurare da ba su san su ba.

A cikin sansanonin ‘yan gudun hijira, yawancin ‘yan mata ba su samu kulawa da buƙatunsu na asali ba wanda hakan ya sa aka yi ta amfani da su ta hanyar yi musu fyaɗe ana ba su kayan tallafi ko abinci.

Yayin da gwamnatin Nijeriya ke samun nasara kan Boko Haram sannu a hankali, wata hanya mai amfani da ake gani don gina zaman lafiya mai ɗorewa a Arewa Maso Gabas ita ce ta hanyar bai wa mata damar samun ci gaba a rayuwarsu.

Mata da yaran da suka tsira daga hare-haren Boko Haram na buƙatar isasshen tallafi don sake farfaɗo da rayuwarsu. Hakan zai taimake su wajen yin aiki tuƙuru da bayar da gudunmawarsu wajen gina zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Hauwa Bello, ‘yar shekaru 65 wacce aka fi sani da Falmata daga garin Gwoza, ta bayar da labarin irin wahalhalun da ta fuskanta a ƙarƙashin ikon Boko Haram. “Ba zan taɓa mantawa da ranar da Boko Haram suka kama Gwoza ba. Wannan ce ranar ƙarshe da na ga ‘ya’yana maza guda biyu,” in ji Falmata.

Ta bayyana yadda mutane suka firgita lokacin da Boko Haram suka shigo garin Gwoza suna ta harbe-harbe, lamarin da ya sa mutane suka fara gudu cikin a firgeci. Duk da gargaɗin da ta yi wa ‘ya’yanta maza bai hana sun fita daga gida cikin ruɗani ba kuma daga nan aka kashe su.

Bayan watanni shidda a ƙarƙashin ikon Boko Haram a garin Gwoza, Boko Haram sun sanar da su cewa sun samu labari mai tushe cewa Sojojin Nijeriya na kan hanyar zuwa don su sake ƙwace garin Gwoza daga hannunsu, don haka suka ce ya zama dole su gudu su bar garin. Falmata, da aka tilasta ta tsere tare da su, ta kwashe watanni ukku a cikin daji kafin ta tsere tare da wasu mata da ƙananan yara.

Sun yi tafiya tsawon kwanaki kafin sojojin Nijeriya suka same su inda suka kai su Sansanin Barikin soja na Giwa Army Barracks a Maiduguri.

Falmata ta kuma bayyana wahalhalun da ta sha a sansanin tare da sauran ‘yan gudun hijira.

“Rayuwa a sansanin da ke a bariki akwai wahala sosai. Da  farko mun samu taimako da kulawa sosai, amma daga baya sai aka yi watsi aka manta da mu. A wasu lokutta sai mun sha wahala wajen samun abinci sau ɗaya a rana, kuma babu magani ga duk waɗanda suka kamu da rashin lafiya.”

Mijin Falmata ya mutu ne sakamakon rashin kulawa da shi daga  zazzaɓin cizon sauro da ba a yi masa magani ba. Ala tilas ta bar sansanin inda ta tsere zuwa Abuja tare da ɗanta guda ɗaya da ya rage. “A wannan shekarun nawa da irin yanayin lafiyata, ba zan iya yin aiki ba. Ɗana ne kaɗai mai kula da mu, kuma yana buƙatar tallafi da damar ci gaba don ya iya kula da mu.”

Falmata Garba, wata matashiya da ta sha wahala a hannun Boko Haram, ta bayyana wa wakilinmu irin yadda ta yi rayuwa da su.

“Sun sace mu ne daga garin Gwoza suka kai mu cikin daji,” in ji Falmata.

Ta ƙara da cewa, “an tilasta mini auren wani daga cikinsu, duk da yake mun haifi yara biyu da shi, amma dukkan yaran sun rasu saboda yunwa da rashin magani.”

A lokacin da ta yanke shawarar tserewa, Falmata ta shirya da wasu yara suka bi dare suka sulale. Sun yi amfani da damar da suka samu ta cewa ’Yan Boko Haram ɗin da suke tsare da su sun fita kai hari wani gari sannan  suka tsere, inda suka kwana ukku suna tafiya cikin jeji. Daga bisani sun haɗu da rundunar sojan Nijeriya wacce ta kai su Maiduguri.

“Amma yanzu gamnati ta kore mu, sun ce mana mu kwashe yanamu-yanamu  mu bar sansanin ’yan gudun hijirar, kuma tun daga wannan lokacin na faɗa tasku. A halin yanzu ina tsaka mai wuya kuma ina neman agaji don in samu in tsira da raina,” In ji Falmata Garba.

Ita ma Hauwa Hamman Gwoza, wata matashiya ‘yar shekara 26, ta ba da labarin abin da ta fuskanta a ƙarƙashin ikon Boko Haram a garin Gwoza. Karatunta ya tsaya cak lokacin da Boko Haram suka mamaye garin, suka ƙona makarantu sannnan suka hana su samun damar yin karatu.

Hauwa an tilasta mata zama a gida tsawon watanni, tana tsoron hukunci ko auren dole idan aka kama ta a waje. Lokacin da Boko Haram suka bar Gwoza, Hauwa ta kasance tare da iyayenta inda aka tilasta su shiga daji tare da mayaƙan Boko Haram. Bayan wasu watanni, ta samu ta tsere, amma ‘yan’uwanta mata biyu suna can tare da Boko Haram, an tilasta musu yin aure da mayaƙan tare da haifar musu yara.

Bayan ta tsere ne ta samu ta yi aure, amma mijinta ya bar ta bayan ta haifi yara huɗu. Yanzu tana zaune ne tare da ɗan’uwanta a sansanin ‘yan gudun hijira na Bwari a Abuja. Hauwa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka mata ta fara kasuwanci domin kula da ‘ya’yanta.

“Kamar yadda kuke gani, ba ni da wata hanyar samun kuɗin shiga sai dai ɗinkin hula da nake yi da hannu, wanda yake ɗaukar kusan wata biyu kafin in kammala guda ɗaya. Ina kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin da abin ya shafa da su taimake ni da jari ko horo na ƙwarewa don in dogara da kaina in kula da yarana.”

A cikin watan Nuwambar bara, Ƙungiyar Kare Haƙƙin bil’Adam ta Amnesty International ta ƙaddamar da wani shiri mai taken #EmpowerOurGirls da nufin jawo hankalin hukumomin Nijeria da sauran masu ruwa da tsaki don tallafa wa mata da ƙananan yaran da suka tsira daga musgunawar ’yan Boko Haram da ta soja a jihohin Arewa maso Gabas don su dogara da kansu.

Daraktan Ƙungiyar Kare Haƙƙin bil’Adam ta Amnesty International a Nijeriya, Isah Sanusi, ya tabbatar wa Aminiya fara aiatar da wannan kamfe tare da yin alƙawarin bayar da cikakken bayani game da shirye-shiryen Amnesty International ke yi don ganin an ba wa mata da ‘yan matan da suka tsira daga Boko Haram tallafin da ya dace.

Sanata Ireagbor, Masanin Tsaro kuma Mai ba da Shawara kan Harkokin Tsaro a Nijeriya ya bayyana cewa, bai wa mata da ‘yan mata da suka tsira daga hare-haren mayaƙan Boko Haram damar samun ayyukan yi da tallafin kuɗi ba kawai wajibi ba ne, wata dabara ce ta yaƙi da ayyukan ta’addanci da a Arewa baki ɗaya.

“Ta hanyar bai wa waɗannan mutanen damar kula da kansu da iyalansu, za mu iya rage tasirin manufofin ‘yan ta’adda waɗanda sau da yawa ke amfani da halin talaucin da mutane ke ciki don yaɗa manufofinsu a cikin al’umma da kuma samun sabbin masu shiga ƙungiyarsu,” in ji Ireagbor.

Ya ƙara da cewa, “a wannan yanayin, matan da aka bai wa dama za su iya zama wakilan sauyi wajen inganta zaman lafiya da daidaito tsakanin maza da mata, da kuma juriya a cikin al’ummominsu.

”Haɗin kai tare da shugabannin al’umma da ƙungiyoyin mata yana da muhimmanci don tabbatar da cewa shirye-shiryen sun dace da al’adun al’umma kuma suna magance ƙalubalen da waɗanda abin ya shafa ɗin ke fuskanta.”

Naomi Abwaku Chibok, Jami’ar Hulɗa da Jama’a na Hukumar Raya Arewa Maso Gabas (NEDC), ta bayyana wa wakilinmu cewa, hukumar tana yin iyakar ƙoƙarinta don tabbatar da cewa mata da ‘yan matan da suka tsira daga Boko Haram a Arewa Maso Gabas ana kula da su da kuma basu damar sake gina rayuwarsu.

“Tare da ƙoƙarin da hukumar ke yi wajen taimakawa matan da suka tsira daga musgunawar Boko Haram ko ta soja, an kafa cibiyar koyon sana’o’i a Ningi Jihar Bauchi. Inda waɗanda abin ya shafa musamman mata suke koyon sabbin hanyoyin sana’a tare da ƙwarewar da za su iya tallafawa rayuwarsu.

“NEDC ta kuma kafa Ɗakin Tiyata don kula da matsalar Yoyon-fitsari ga mata da ke buƙatar hakan,” in ji Naomi.

Da muka tuntuɓe ta, ta hanyar manhajar WhatsApp, Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Borno, Hajiya Zuwaira Gambo, ta bayyana cewa ba za ta iya yin tsokaci ba saboda yanayin lafiyarta.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matar gwamna ta ɗauki nauyin ragon suna da hidimar duk matar da ta haifi ’yan uku a Sakkwato
  • Matan da suka tsira daga Boko Haram na buƙatar tallafin musamman
  • Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kona Yara Da Mata A Harin Da Suka Kai Khum Yunis Na Gaza
  • AGILE: Gwamnatin Kaduna da Bankin Duniya Na Sauya Rayuwar ’Ya’ya Mata Ta Hanyar Ilimi
  • Yara Kimani 3,500 Ne Suka Rasa Rayukansu A Taken Medeteranin A Shekaru 10 Da Suka Gabata
  • MDD Ta Nuna Damuwarta Akan Kokarin Sake Raba Kasar Sudan Gida Biyu
  • Najeriya da gwamnatin sojin Nijar da Nijar sun sasanta
  • Batawa Sin Suna Ba Zai Taimaka Kawar Da Tambarin Amurka A Matsayin Daular Kutsen Intanet Ba
  • Gwamnatin Kano Za Ta Sake Buɗe Makarantun Kwana 10 Don Inganta Ilimin Yara Mata
  • Kokarin Da Iran Take A Tattaunawa Da Amurka Shi Ne Dage Mata Takunkuman Zaluncin Da Aka Dora Mata