Ƙungiya ta raba wa marayu da mabuƙata kayan makaranta a Kano
Published: 26th, February 2025 GMT
Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta.
Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi.
Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabinoSakataren ƙungiyar, Kwamared Usman Bello Kofar Mata, ya ce sun bayar da taimakon ne, domin rage yawan yara da ke gararamba a tituna, musamman marayu.
“Mun ga yadda wasu yara ke shiga tsaka mai wuya bayan rasuwar iyayensu.
“Wasu ba su da kowa da zai kula da su, sai dai su riƙa yawo kamar awaki. Don haka, muka yi bincike muka zaƙulo irin waɗannan yara don mu taimaka musu,” in ji shi.
Taron rabon kayayyakin ya samu halartar mai unguwar Kofar Mata, Alhaji Muhammad Jibril, wanda ya yi kira da a riƙa taimakon marayu da mabuƙata domin hana lalacewar tarbiyyar yara a yankin.
Ya ce rashin irin wannan taimako ne ke janyo koma-baya a yankin Arewa, inda ya bayar da misali da Kudancin Najeriya inda ake ɗaukar nauyin marayu har su girma su zama mutane nagari a rayuwa.
“Idan har ba a taimaka wa marayu da mabuƙata ba, za su tashi babu tarbiyya.
“Idan yaro ba shi da gata, babu wanda zai gyara masa hanya. Amma idan ana tallafa masa, zai girma da sanin darajar rayuwa,” in ji shi.
Ya buƙaci iyaye da al’umma su ci gaba da kula da tarbiyyar yara tare da basu kulawa da taimako domin su zama mutane nagari da za su amfanar da al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kayayyakin Makaranta Kofar Mata Ƙungiya Marayu
এছাড়াও পড়ুন:
Gobara Ta Ƙone Sabon Ginin Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Mata Na Jami’ar Sokoto
Babu wata ɗaliba da ke cikin ginin a lokacin da gobarar ta tashi, domin tuni aka sauya wa ɗaliban masauki bisa umarnin jami’ar.
Har yanzu dai hukumomi ba su bayar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp