Aminiya:
2025-04-19@09:18:17 GMT

Buhari da El-Rufai ba su halarci babban taron APC ba

Published: 26th, February 2025 GMT

Jam’iyyar APC mai mulki, ta gudanar da babban taronta na ƙasa a Abuja, wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar daban-daban.

Duk da kasancewar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima a waje taron, wasu manyan shugabannin jam’iyyar ba su halarci taron ba.

Ƙungiya ta raba wa marayu da mabuƙata kayan makaranta a Kano Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa

Daga cikin waɗanda ba su halarci taron ba akwai tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, da tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi.

Dalilin Rashin Halartar Buhari

Dangane da dalilin da ya sa Buhari bai samu halartar taron ba, tsohon mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa tsohon shugaban bai samu katin gayyata a kan lokaci ba.

“Taron masu ruwa da tsaki ne, wanda ya kamata Buhari ya halarta. Amma an aike masa da gayyatar taron ne a ranar Litinin, sai dai bai samu wasiƙar ba sai ranar Talata da rana.

“A wannan lokacin, ba zai iya barin Daura ya tafi Abuja don halarta ba, ko da kuwa yana da jirginsa na musamman.”

Duk da hakan, Garba Shehu ya jaddada cewa Buhari har yanzu cikakken ɗan jam’iyyar APC ne kuma zuciyarsa tana tare da ita.

Dalilin Rashin Halartar El-Rufai da Amaechi

Babu cikakken bayani game da dalilin da ya sa Malam Nasir El-Rufai bai halarci taron ba.

Sai dai a baya, tsohon gwamnan na Kaduna ya sha bayyana rashin jin daɗinsa game da jagorancin jam’iyyar, inda zargi cewa ta sauka daga aƙidar da aka kafa ta.

Duk da haka, ya nanata cewar har yanzu shi cikakken ɗan jam’iyyar.

Shi ma Rotimi Amaechi bai bayyana dalilin rashin halartarsa ba.

A kwanakin baya dai, tsohon gwamnan na Ribas ya daina yawan magana a fili.

A wata hira da ya yi da BBC, ya ce: “Idan akwai abu guda ɗaya da na koya daga Shugaba Buhari, shi ne rage yawan surutu.

“Domin ya taba fada min cewa ‘Amaechi, ba don abinci kawai aka yi ciki ba.’“

Manyan Jiga-Jigan da Suka Halarci Taron

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai na jihohin Edo, Benuwe, Ondo, Ekiti, Kaduna, Jigawa, Nasarawa, Yobe, Nejs, Legas, Kogi, Ogun, da Imo.

Mataimakin gwamnan Ebonyi da wasu tsofaffin gwamnoni daga Kogi, Kebbi, Neja, Zamfara, da Filato su ma sun halarci taron.

Duk da rashin halartar wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar, babban taron ya gudana kamar yadda aka tsara.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Buhari jam iyya taro tsohon gwamnan halarci taron babban taron

এছাড়াও পড়ুন:

Saudiyya da Iran sun jaddada aniyar fadada alakar soji a tsakaninsu

Iran ta jaddada shirinta na fadada huldar soji da kasar Saudiyya a wani bangare na batutuwan da ziyarar ministan tsaron kasar Saudiyya Tehran ta kunsa.

Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Bagheri ya shaidawa Yarima Khalid bin Salman a Tehran a wannan Alhamis cewa “Kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu da sojojinsu za ta kawo yanke kauna ga makiyanmu da kuma sanya farin ciki ga abokanmu da sauran musulmi”.

Bagheri ya godewa Saudiyya a kan halartarta a matsayin mai sa ido a babban atisayen sojojin ruwa na tekun Indiya (IONS), wanda aka fi sani da IMEX 2024.

Iran, Rasha, da Oman ne suka gudanar da atisayen a tekun Indiya, tare da halartar tawagogin masu sa ido daga kasashe da dama da suka hada da Saudiyya, Indiya, Thailand, Pakistan, Qatar, da Bangladesh.

Yarima Khalid ya bayyana godiyarsa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma babban hafsan sojin kasar bisa kyakkyawar tarba da suka yi masa tare da tawagarsa a birnin Tehran, yana mai cewa: “karamcin da kuk a yi mana  yana nuna kyakkyawar alaka mai karfi da ke tsakaninmu”.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Abdulrazaq Ya Bukaci Kiristoci Da Su Tuna Da Darussan Lokacin Ista
  • Bankin Zenith Ya Samu Ribar Naira Tiriliyan 3.97
  • 2027: Dalilan Da Suka Sa ‘Yan Siyasa Ke Tururuwar Zuwa Gidan Buhari A Kaduna
  • Ya kashe masoyin tsohuwar matarsa bayan sakinta a Neja
  • PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike
  • BUK Ta Shirya Taron Na Shekara-shekara Akan Malam Aminu Kano
  • Saudiyya da Iran sun jaddada aniyar fadada alakar soji a tsakaninsu
  • Tsohon Minista Ya Zargi Isra’ila Da Kasashen Yammacin Turai Da Kitsa Kashe-kashen Rayuka A Nijeriya 
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Garambawul A Fannin Kiwon Lafiya
  • Majalisa ta gayyaci Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas