Gwamnatin Jigawa Za Ta Biya Diyar Sama Da N1.5 Biliyan Ga Wadanda Aikin Tituna Ya Shafa
Published: 26th, February 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin gari ya shafa.
Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse.
A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na yanki suka gabatar.
Ya ce, majalisar ta kuma amince da kashe sama da naira biliyan takwas da miliyan dari biyu a matsayin kashi 30 bisa na kudaden shirin noman rani na shinkafa na shekarar 2025.
Ya kuma yi bayanin cewa, an amince da hakan ne da nufin samar da wadataccen abinci da inganta rayuwar miliyoyin al’ummar Jigawa ta hanyar bai wa Manoma 58,500 rance, don noma hekta 50,000 na shinkafa a fadin yankunan da ake noman shinkafa, kamar yadda ma’aikatar noma da albarkatun kasa ta gabatar.
Kwamishinan ya ce, majalisar zartaswa ta jihar ta kuma amince da sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita wa’adin shekaru 2 tsakanin ma’aikatar lafiya ta gwamnatin jihar Jigawa da kungiya mai zaman kanta ta Medicins San Frontiers (MSF) da ke kasar Faransa.
A cewarsa, rattaba hannu kan yarjejeniyar na da nufin karfafa kokarin jihar na rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, ta hanyar samar da ingantacciyar kula ga masu juna biyu a babban asibitin Jahun da kuma cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na Miga da Ajura.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dokokin Zamfara Ta Dawo da Dan Majalisa Basko da Aka Dakatar
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta mayar da dan majalisar dokokin jihar Zamfara da aka dakatar, Shamsudeen Hassan Basko, mai wakiltar mazabar Talata Mafara ta Arewa, bayan da ya nemi gafarar majalisar.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da sakataren yada labaran majalisar Bello Madaro ya raba wa manema labarai a Gusau.
A zaman da aka yi, Kakakin Majalisar, Alhaji Bilyaminu Ismail Moriki, ya karanta abin da ke cikin wasikar neman afuwar Basko, inda daga nan ne ya nemi shawarar majalisar ta gamayya inda ‘yan majalisar suka amince da dage dakatarwar.
Shugaban majalisar ya jaddada bude kofar majalisar na karbar irin wasikun neman afuwa daga sauran ‘yan majalisar bakwai da aka dakatar, inda ya ce irin wadannan matakai za su ba su damar dawo da su tare da samar da hadin kai a cikin majalisar.
Mambobin sun kuma yi masa maraba da komawa zauren majalisar, sannan sun bukaci sauran mambobin da aka dakatar da su yi koyi da ayyukansa domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban mazabarsu da jihar baki daya.
A takaitacciyar jawabinsa, Shamsudeen Hassan Basko ya bayyana matukar godiya ga majalisar bisa damar da ta samu ta mayardashi.
Basko ya yi alkawarin ci gaba da bin ka’ida, da’a na Majalisar, ya kuma sha alwashin nisantar da kansa daga duk wata kungiya ko yin tasiri da ke yunkurin bata mutunci da ikon majalisar.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar 26 ga watan Fabrairun 2024 ne majalisar, bayan wani kudiri da shugaban masu rinjaye, Bello Mazawaje ya gabatar, ta dakatar da mambobinta takwas bisa saba wa kundin tsarin mulkin majalisar (Oda 10, Doka ta 9).
Matakin ladabtarwar dai ya samo asali ne daga zarge-zargen da ake yi masa, wanda ya hada da shigar karfi da yaji a ofishin magatakarda da zama ba bisa ka’ida ba, da dakile ayyukan majalisa, da kuma gudanar da ayyukan da ake ganin bai dace da ‘yan majalisar ba.
REL/AMINU DALHATU.