Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno
Published: 26th, February 2025 GMT
’Yan Ta’addan Boko Haram sun kai hari ƙauyen Kaleri da ke Ƙaramar Hukumar Jere a Jihar Borno, inda suka sace mutum biyu da kayan abinci masu tarin yawa.
Wata majiya daga yankin ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne kusa d Jami’ar Maiduguri (UNIMAID).
Buhari da El-Rufai ba su halarci babban taron APC ba Ƙungiya ta raba wa marayu da mabuƙata kayan makaranta a KanoMajiyar ta ce, “Sun shigo da manyan makamai, suna harbe-harbe suna bi gida-gida don neman kayan abinci, suna sanya tsoro a zukatan mazauna garin.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Sun yi garkuwa da mutane biyu, sannan suka kwashe kayan abinci.”
Bayan faruwar lamarin, jami’an ’yan sanda sun rufe yankin tare da kama wasu mutane, amma ba su bayyana cewar waɗanda suka kama na da alaƙa da harin ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram Garkuwa Kayan abinci Ƙauye kayan abinci
এছাড়াও পড়ুন:
Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu
Wani jariri sabuwar haihuwa ya riga mu gidan safiyar Litinin bayan mahaifiyarsa ta jefo shi ta tagar wani otel a birnin Paris. Jami’an tsaro da ke shigar da ƙara sun ce an tsinci gawar jaririn wanda ko cibiyarsa ba a yanke ba. An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini Wata majiya ta ce uwar jaririn mai shekaru 18 ta jefo shi ne ta tagar ɗakin wani otel daga hawa na biyu a Kudancin Faransa. An bai wa jaririn kulawar gaggawa amma a ƙarshe ya ce ga garinku nan kamar yadda majiyar ta tabbatar. ’Yan sanda sun ce jaririn ya mutu da misalin ƙarfe 7:45 na safiya agogon GMT a Asibitin Debre kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito.Bayanai sun ce uwar jaririn wadda ɗaliba ce ’yar asalin ƙasar Amurka ta jefo jaririn ne bayan haihuwarsa a ɗakin da ke hawa na biyu na otel ɗinTuni dai mahukunta a Faransa suka ƙaddamar da bincike kan lamarin yayin da suka tabbatar da cafke matashiyar da ake zargi.
An ruwaito cewa BaAmurkiyar na daga cikin tawagar wasu matasan ɗalibai da ke yawon ƙaro ilimi a nahiyar Turai.
A halin yanzu dai an kai matashiyar asibiti domin samun kulawar da ta dace a sanadiyar haihuwar da ta yi a yayin da bincike zai ci gaba da gudana.
AFP