An shawarci majalisar dokokin kasar da su mai da hankali kan ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kasar nan domin inganta shugabanci nagari.

Masu kiran waya a shirin “KAKAKI” na gidan Rediyon Najeriya Karama FM ne suka bada shawarar hakan a lokacin da suke ba da tasu gudunmawar a kan batutuwan da suka shafi kasa.

Sun bayyana damuwarsu kan rahotannin karar da wata sanata daga jihar Kogi, Natasha Akpoti, ta shigar kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, biyo bayan  zargin bata suna.

Alhaji Ibrahim Alaramma, Idris Adamu Danfulani, da Sani Batira sun jaddada bukatar shugabannin majalisar su tabbatar da kafa doka mai inganci don yaki da talauci da rashin tsaro.

Shi ma da yake jawabi, wani bako a shirin, Alhaji Suleiman Muhammad ya yi kira ga gwamnati da ta kara samar da ayyukan raya kasa da ababen more rayuwa kamar yadda ake yi a kasashen da suka ci gaba.

 

Suleiman Kaura

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kotun Tarayya Ta Dakatar Da Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Daga Tsige Honarabul Ango

Babbar kotun tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara ta dakatar da majalisar dokokin jihar daga tsige Honarabul Aliyu Ango Kagara, dan majalisar APC mai wakiltar mazabar Talata Mafara ta Kudu.

A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan wata kara mai lamba FHC/GSCS/10/2025 da Kagara ya shigar kan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara,  da Kakakinta, da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

Ta ce shari’ar da mai shari’a Salim Olasupo Ibrahim ya jagoranta ta kalubalanci tsige Kagara da shugabannin majalisar suka yi.

A cewar sanarwar, kotun ta bayar da umarnin wucin gadi na hana INEC gudanar da zaben cike gurbi na mazabar Talata Mafara ta Kudu, wanda Kagara ke wakilta a halin yanzu.

Mai shari’a Olasupo ya kuma bayar da umarnin tsayawa kan wannan hukunci har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron karar da aka shigar a gaban kotu.

An dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Maris na 2025.

A halin da ake ciki, majalisar dokokin jihar Zamfara ta dakatar da ‘yan majalisa 9 da suka fito daga jam’iyyu daban daban, lamarin da ya rage yawan mambobinta da ke kasa da kashi biyu bisa ukun da ake bukata wajen zartar da kudiri.

Duk wata doka da aka zartar a ƙarƙashin wannan yanayi, ana iya ɗaukarta sabawa tsarin mulki.

 

Daga Aminu Dalhatu

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sheikh Na’im Kasim Ya Gana Da Ministan Harkokin wajen Kasar Iran Da Shugaban Majalisar Dokoki
  • El-rufa’i Ba Zai Halarci Taron Jam’iyyar APC Na Kasa Ba, Kuma Ganduje Na Nan A Shugabanci 
  • Shugabannin Afirka Ta Kudu, Malaysia Da Colombia Sun Yi Kira Da A Kawo Karshen Laifukan Isra’ila
  • Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio
  • Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa
  • Kar A Ji Tsoron Aikace-Aikacen Kasar Amurka
  • Kotun Tarayya Ta Dakatar Da Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Daga Tsige Honarabul Ango
  • Da Ɗumi-ɗumi: NNPP Ta Dakatar Da Sanata Kawu Sumaila Da Wasu ‘Yan Majalisa Uku
  • Iran ta yi Allah wadai da keta hurumin kasar Lebanon da Isra’ila ta yi