Sheikh Na’im Kasim Ya Gana Da Ministan Harkokin wajen Kasar Iran Da Shugaban Majalisar Dokoki
Published: 26th, February 2025 GMT
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kasim ya gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arigchi da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon.
Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Jami’an gwomnatin 2 sun je kasar Lebanon ne don halattan taron Jana’izar manya-manyan shahidan kungiyar kuma shuwagabannin kungiyar, Shahid Sayid Hassan Nasarallah, da kuma magajinsa Sayid Hashin Safiyyuddeen.
Labarin ya kara da cewa jakadan kasar Iran a Lebanon Mujtaba Amani ya sami halattan taron inda bangarorin suka tattauna sabbin al-amura da suke tasowa a kasar da kuma yankin kudancin Asiya da kuma al-amura da suke faruwa a duniya gaba daya.
A cikin jawabin da ya gabatar a taron jana’izar dai, sheikh Qasim ya bayyana cewa kungiyar Hizbullah zata ci gaba a kan tafarkin Shahid Hassan Nasaralla. Sannan al-amura da dama sun sauya, don haka zasu yi aikin bisa abinda suka ga ya dace a ko wani lokaci.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ranar Kudus: al’ummar Iran zasu nuna hadin kan su ga duniya_ Pezeshkian
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kira ga al’ummar kasar da su nuna hadin kai a yayin bukukuwan ranar Kudus ta duniya wato ranar JUma’ar kashe ta watan Ramadana da ke gabatowa, yana mai jaddada cewa hakan zai nuna matukar goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga al’ummar Falastinu.
Pezeshkian, ya bayyana hakan ne a yayin taron majalisar ministocin kasar na farko sabuwar shekarar kalandar farisa, inda yake cewa “Ina fatan tare da halartar al’ummar kasar, za a gudanar da ranar Kudus mai daraja, kuma a wannan rana al’umma za su nuna hadin kai ga duniya.”
Ranar Kudus ta duniya dai marigayi Imam Khumaini ne ya ayyana ta kuma ana gudanar da ita a kowace shekara a ranar Juma’ar karshe ta azumin watan Ramadan domin nuna goyan baya ga al’ummar falasdinu.
Ta kasance wani gangami na duniya ga musulmi da masu neman ‘yanci a wajen bayyana goyon bayansu ga al’ummar Falastinu tare da yin Allah wadai da mamayar da gwamnatin Isra’ila ke yi wa yankunan Falastinawa da kuma cin zarafin da take yi wa masallacin Kudus.