Hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ta kaddamar da kayakin aikin da ake bukata don samar da garin sinadarin (Tellurium Dioxide) wanda ake hada maganin cutar daji wanda ake kira (Iodine-131) da shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar hukumar makamashin nukliyar ta Iran, na cewa ana samar da wannan sinadarin ne tare da amfani da makamashin nukliya.

Kuma a halin yanzu kasar Iran zata iya samar da maganin wanna cutar a cikin gida. Labarin ya kara da cewa, idan JMI ta fara samar da maganin, zata bar dogaro da kasashen wajen don magance cutar a cikin gida, sannan wata dama ce ta samun kudaden shiga daga kasashen waje. Don haka a halin yanzu Iran tana da damar samar da maganin cutar mai suna  Iodine-131 a cikin gida. Kafin haka dai kasashe kadan ne suke da fasahar samar da wannan maganin a duniya, kuma da tsada.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: samar da maganin

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kaduna za ta ɗauki ma’aikatan lafiya 1,800 aiki

Gwamnatin Jihar Kaduna, ta sanar da shirin ɗaukar ma’aikatan lafiya 1,800 aiki don inganta tsarin Kiwon Lafiya a Matakin Farko (PHC) a faɗin jihar.

Wannan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin ma’aikata da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar.

Ƙungiyar JNI ta raba wa marayu 50 kayan Sallah a Borno An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara

Kamar yadda Kwamishiniyar Lafiya, Hajiya Umma Ahmad, ta bayyana, wannan mataki zai taimaka wajen rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da yara.

“Wannan mataki zai cike giɓin da ake da shi a cibiyoyin lafiya, domin tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Kaduna,” in ji ta.

Gwamnatin jihar ta fara gyara cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 255 tare da samar da kayan aiki na zamani da magunguna.

Wannan zai bayar da damar kula da cututtuka kamar su ciwon suga, hawan jini, da kuma bayar da agajin gaggawa ga mata masu naƙuda.

“Ingantaccen kiwon lafiya ba gata ba ne, haƙƙi ne,” in ji Hajiya Umma, yayin da ta ke jadadda ƙudirin gwamnatin jihar kan kiwon lafiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Kaduna za ta ɗauki ma’aikatan lafiya 1,800 aiki
  • Cutar sanƙarau ta yi ajalin mutum 3 a Gombe
  • Duk Da Dokar ‘Yancin Samar Da Abinci: Yara Miliyan 11 Na Fama Da Ƙaranci Abinci A Nijeriya
  • Iran Ta Gudanar Da Faretin Jiragen Ruwa A Tekun Farisa Da Kuma Tekun Caspian Don Raya Ranar Kudud Ta Duniya
  • Iran Ta Bada Amsa Ga Wasikar Shugaban Kasar Amurka Ta Gayyatar Kasar Zuwa Tattaunawa Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
  • Gwamnatin Amurka Tana Shirin Dakatar Da Bada Kudaden Tallafi Don Samar Da Wasu Magunguna
  • Ina Mafita Game Da Ƙalubalen Ƙarancin Abinci A Nijeriya
  • Karfin Lantarki Da Tashoshi Masu Amfani Da Makamashi Mai Tsafta Ke Samarwa A Sin Ya Kai Kilowatt Biliyan 2
  • Sabbin Nasarorin Rigakafi Da Warkar Da Cutar TB Na Kasar Sin Sun Kara Kuzarin Dakile Yaduwarta Duniya 
  • Kwalara Ta Kashe Mutum 14, Ana Zargin 886 Sun Kamu A Nijeriya – NCDC