Ɗangote Ya Rage Farashin Man Fetur Saboda Gabatowar Azumi
Published: 26th, February 2025 GMT
Sakamakon wannan ragin da aka samu, yanzu gidan mai na MRS zai sayar da man a jihar Legas a kan naira 860, sai mutanen da suke yankin kudu maso yamma kuma da za su saya a kan naira 870, sai kuma mutanen Arewa da za su saya a kan naira 880, sai mutanen kudu maso kudu da kudu maso gabas da za su saya akan naira 890.
Kamfanin ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su taimaka wajen ganin sauƙin ya je inda ake bukata, domin an yi ragin ne don sauƙaƙawa al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Matatar Dangote Matatar Mai
এছাড়াও পড়ুন:
Jagora Ya Yi Kira Ga Iraniyawa Su Fito Don Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zargar Ranar Kudus Ta Duniya
Imam sayyid Aliyul Khamina’ie Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran yayi kira ga mutanen kasar su fito kwansu da kwarkwatansu don halattar zanga-zangar ranar Kududs ta duniya a yau Jumma’a.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Alhahamis da yamma. Ya kuma kara da cewa fitowar zanga-zangar ranar Kudus ta duniya alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, sannan cika alkawali ne ga al-ummar kasar Falasdinu kan cewa mutanen kasar Iran ba zasu taba barinsu su, su kadai ba.
Ranar Qudus ta duniya dai, rana ce wacce Imam Khomaini (q) wanda ya kafa JMI ya ware a ko wace ranar Jumma’a ta karshe na watan Ramadan mai alfarma, na ko wace shekara, don nuna goyon bayan ga al-ummar Falasdinu wadanda ake zalunta, saboda mamayar kasarsu da aka yi. Sannan da kasancewar masallacin Al-Aksa a birnin Qudus al-kiblar musul ce da farko, wanda yake hannun yahudawan sahyoniyya a halin yanzu.
A bana wannan zanga-zangar za’a yi ta ne a dai-dai lokacinda yahudawan suke kissan kiyashi wa falasdinawa a Gaza a karkashin yakin tufanul aksa, wanda ya zuwa yanzu sun kashe falasdiyawa fiye da dubu 50 a yaynsa wasu fiye da dubub 120000 suka ji raunin..