Sin Ta Yi Allah Wadai Da Taimakon Soji Da Amurka Ke Bai Wa Taiwan
Published: 27th, February 2025 GMT
A yau Laraba, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina bai wa Taiwan makamai, ta kuma guji yin kafar ungulu ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin Taiwan.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa kullum, lokacin da aka tambaye shi game da rahotannin da ke cewa, gwamnatin Trump ta bayar da dalar Amurka biliyan 5.
A cewar Lin, Sin ta damu matuka game da ire-iren wadannan rahotanni, yana mai nuni da cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana jaddada adawa da taimakon soja da Amurka ke bai wa yankin Taiwan na kasar Sin, saboda irin wannan hali ya saba wa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” da kuma sanarwar hadin gwiwa guda uku wadanda Amurka da Sin suka fitar, tare da keta ‘yancin kan kasar Sin da muradunta na tsaron kasa, kuma hakan na aikewa da mummunan sako ga dakarun ‘yan aware masu neman wai ‘yancin kan Taiwan. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Da NSA Ribadu Ba Abokaina Ba Ne — El-Rufai
Ya kuma zargi NSA da nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2031, don haka yake kokarin kawar da duk wanda zai zamar masa kalubale a kan hanyarsa.
Cikakken bayani na nan tafe…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp