Gwamnatin Jigawa Ta Biya Sama Da Naira Miliyan 730 Ga Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya
Published: 27th, February 2025 GMT
Hukumar fansho ta jihar Jigawa da kananan hukumomin jihar ta fara biyan sama da naira miliyan 733 ga ma’aikata sama da 280 da suka yi ritaya da kuma ‘yan uwan ma’aikatan da suka rasu.
Shugaban hukumar Dakta Bilyaminu Shitu Aminu ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga wadanda abin ya shafa a ofishin fansho da ke Dutse babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa kudaden sun hada da na barin aiki, da na ma’aikatan da suka mutu.
A cewarsa, ma’aikatan 281 sun hada da na jiha, da kananan hukumomi da na hukumar ilimi, wadanda suka yi ritaya na son rai ko kuma sun kai shekarun ritaya ko kuma wadanda suka mutu suna aiki.
Dakta Bilyaminu Shitu ya ci gaba da bayanin cewa za a biya ma’aikata 208 da suka yi ritaya daga aiki sama da naira 542, yayin da za a biya sama da Naira miliyan 144 ga ‘yan uwan wadanda suka mutu a bakin aiki su 47.
A cewarsa, rukunin karshe su ne ma’aikata 26 da suka yi ritaya daga aiki kuma suka fara karbar fansho duk wata amma sun mutu kafin su kai wa’adin mafi karancin shekaru biyar bayan sun yi ritaya.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa jihar Jigawa na daya daga cikin jihohin da ke da kyakkyawan tsarin fensho mafi inganci a kasar nan, duba da yadda ta ke kokarin biyan wadanda suka yi ritaya ba tare da wata matsala ba kuma akan lokaci.
Ya ce wannan gagarumin ci gaba ya nuna irin yadda gwamnatin jihar ta himmatu wajen kyautata rayuwar ‘yan fanshonta da kuma muhimmancin tabbatar da biyan hakkokin wadanda suka yi wa jihar hidima.
Shugaban ‘yan fanshon ya ce, hukumar ta jajirce wajen tabbatar da biyan kudaden fansho cikin lokaci da inganci kuma tana sa ran za ta ci gaba da yin sabbin abubuwa da nufin inganta jin dadin ‘yan fanshonta.
Biyan kudaden da aka gudanar a hedikwatar hukumar fansho ta jihar Jigawa dake Dutse, wani bangare ne na kokarin karrama kwazon ma’aikatan gwamnati da suka sadaukar da kai wajen yi wa jihar hidima.
Shugaban hukumar ya kuma yabawa Gwamna Malam Umar Namadi bisa irin goyon bayan da yake bai wa hukumar.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, wadanda aka biya hakkokin nasu, sun nuna jin dadinsu da yadda aka biya su akan lokaci.
Sun yi nuni da cewa, biyansu kudaden zai ba su damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu da kuma inganta rayuwarsu a lokacin ritaya.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa da suka yi ritaya wadanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
Sallah: Hadimin gwamnan Sakkwato ya bai wa magoya bayan APC kyautar N22m
Mai Bai Wa Gwamnan Sakkwato Shawara kan Harkokin Karkara, Malami Muhammad Galadanchi (Bajare), ya bai wa magoya bayan jam’iyyar APC a jihar, kyautar Naira miliyan 22 domin gudanar da shagalin Sallah Karamar.
Yayin bayar da kyautar a ranar Alhamis, Bajare ya ce ya yi hakan ne domin nuna godiyarsa ga jagoran APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, da Gwamna Ahmad Aliyu, bisa damar da suka ba shi don ba da gudunmawarsa ga ci gaban jihar.
An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Isuhu Yellow a Zamfara Hadimin Gwamnan Kano Tanka Galadanci ya rasu“Wannan tallafi saƙon godiya ne daga shugabanninmu zuwa gare ku. Idan ba su ba mu dama ba, ba za mu iya wannan ba.
“Kuma muna shirye mu ƙara tallafawa a duk lokacin da buƙata hakan ta taso,” in ji shi.
Ya jinjina wa al’ummar Ƙaramar Hukumar Sakkwato ta Arewa, bisa sadaukarwar da suka yi wajen ganin jam’iyyar APC ta yi nasara, inda ya ce hakan ne ya sa suka cancantar a yi masu hidima.
Bajare, ya tabbatar da cewa zai ci gaba da tallafa wa magoya bayan jam’iyyar lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da ci gaban tafiyar siyasarsu.
Dangane da tsarin rabon tallafin, ya ce kowane mutum da aka zaɓa zai amfana da kuɗi tsakanin Naira 100,000 zuwa miliyan ɗaya, ya danganta da matsayinsa.
Haka kuma ya yi fatan al’umma za su gudanar da shagalin sallah cikin lumana da kwanciyar hankali.