Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce Gwamna Umar Namadi ya amince da nadin sabbin jami’an cibiyoyi 27 da za su gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025.

Babban Daraktan Hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar.

Ya ce, an zabo sabbin jami’an cibiyar ne daga dukkan kananan hukumomin jihar 27, kuma za su samu horo da jagoranci kan ayyukan da hukumar ta dora musu.

Ya kuma bayyana cewa, tuni hukumar ta gudanar ta taron bita ga dukkan jami’an shiyyar da nufin sanar da jami’an irin ci gaban da aka samu a shirye-shiryen gudanar da aikin hajji mai zuwa.

Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ake ci gaba da gudanar da harkokin ilimantar da Alhazan game da aikin hajjin.

Ya yi bayanin cewa, an tanadar da  zababbun malaman addinin Islama domin gudanar da aikin bita ga Alhazai da ke gudana a babban masallacin Dutse.

Ya  ce, hukumar jin dadin Alhazai ta jihar ta bullo da sabbin dabaru na ilmantar da Alhazan na bana.

Ya shawarci maniyyata musamman wadanda wannan ne Hajjinsu na farko, da su yi amfani da wannan dama wajen inganta iliminsu na  addini da sauran muhimman bayanai da za su taimaka musu wajen gudanar da aikin hajji karbabbe.

Shugaban ya ce, nan ba da jimawa ba za a rufe  gudanar da taro bitar  har sai bayan watan Ramadan.

Ya ce, taron bitar da hukumar ta gudanar, ya bai wa maniyyatan jihar damar samun ilimin aikin hajji da kuma sanin tsare-tsaren da hukumomin Saudiyya da hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON suka tanadar a aikin hajjin bana.

Don haka, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya yaba wa mahalarta taron bitar, inda ya kara da cewa hakan karin ilimi ne da zai amfane su baki daya.

Da yake tsokaci game da rajistar da ake ci gaba da yi a jihar, shugaban hukumar ya yi kira ga maniyyatan da suka fito daga dukkan kananan hukumomi ashirin da bakwai na jihar da har yanzu ba su kammala biyan kudin ba, su yi kokarin cikawa domin hukumar  NAHCON ta kara wa’adin biyan kudin zuwa mako mai zuwa.

Labbo, ya ce ranar wa’adin zai cika ne a ranar 7 ga watan Maris 2025, inda ya kara da cewa, hukumar ta biya kusan Naira biliyan 6 ga NAHCON.

Ya kuma yabawa jami’an shiyyar da suka yi rijista, tare da tattara kudaden ajiyar hajji a yankunansu.

Shugaban hukumar, ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa amincewa da sabbin jami’an cibiyar da kuma goyon baya da hadin kai da ake ba hukumar a kowane lokaci.

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa gudanar da aikin

এছাড়াও পড়ুন:

Sabbin Nasarorin Rigakafi Da Warkar Da Cutar TB Na Kasar Sin Sun Kara Kuzarin Dakile Yaduwarta Duniya 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wike Ya Jinjina Wa Tinubu kan Bunkasa Ilimi Mai Zurfi
  • Gwamna Abba Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Jarumi Karkuzu
  • Kamun Akanta-janar Take-taken Toshe Bakin Gwamnan Bauchi Ne – Ƙungiya
  • Za a Fara Cin Moriyar Shirin BEAR III Na UNESCO da Koria Ta Kudu Jihar Kano
  • Lakurawa sun kashe jami’an Kwastam 2 a Kebbi
  • Kwara Ta Gargadi Jama’a Akan Gine-Gine Akan Bututun Ruwa
  • NLC a Zamfara sun Bada Wa’adin Kwanaki 14 a Aiwatar da Mafi Karancin Albashi
  • NAJERIYA A YAU: Halin Da Matasa Suka Tsinci Kansu A Najeriya
  • Sabbin Nasarorin Rigakafi Da Warkar Da Cutar TB Na Kasar Sin Sun Kara Kuzarin Dakile Yaduwarta Duniya 
  • Hukumar IAEA ta yi ishara da yiwuwar sake komawa teburin tattaunawa tare da Iran