HausaTv:
2025-04-18@23:17:56 GMT

Trump Ya Kawo Karshen Shirin Bunkasa Samar Da Wutar Lantarki A Afirka

Published: 27th, February 2025 GMT

Gwamnatin Donald Trump ta kawo karshen wani shirin Amurka na bunkasa samar da wutar lantarki a Afirka, wanda aka kaddamar fiye da shekaru 10, in ji Bloomberg.

Shirin wanda tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kaddamar a shekarar 2013, yana da nufin samar da wutar lantarki ga miliyoyin gidaje a nahiyar Afirka, wanda Hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) ke tafiyar da shi.

Wannan na daga cikin shirin Trump na rage kashe kudade na tarayya wanda ma’aikatar ingancin gwamnati ke jagoranta.

Kusan dukkanin manufofin shirin “Power Africa” ​​an sanya su cikin jerin shirye-shiryen da za a kawar da su.

A ranar 20 ga watan Janairu, ne shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka ta dakatar da tallafin da Amurka ke bayarwa, wanda kungiyoyi masu zaman kansu da dama suka dogara da da shi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Hamas ta bukaci hadin kan duniya domin kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira ga al’ummar duniya da su ba da himma wajen shiga wani gangami na tsawon mako guda domin ganin an kawo karshen mummunan yakin da Isra’ila ke yi na kisan kiyashi a zirin Gaza da aka yi wa kawanya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar yau Laraba, Hamas ta yi kira ga “kasashen Larabawa da na musulmi da kuma ‘yantattun mutane” na duniya da su halarci gangamin na ranakun Juma’a, Asabar da Lahadi (18, 19 da 20 ga Afrilu).

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta ayyana wadannan ranaku a matsayin “ranakun nuna fushin duniya dangane da mamaya.”

Hamas ta sake nanata bukatar daukar matakin gaggawa na kasa da kasa don kawo karshen “ci gaba da cin zarafi da kisan kiyashin da yahudawan sahyoniya suka yi wa al’ummar Falasdinawa a Gaza, wanda ke gudana a karkashin goyon bayan Amurka da kuma shiru na kasa da kasa.”

Har ila yau, ta yi kira da a gudanar da yajin aikin gama-gari a ranar Talata 22 ga watan Afrilu a dukkan jami’o’i da cibiyoyin ilimi na duniya domin tallafawa al’ummar Gaza da aka yi wa kawanya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka Na Shirin Rufe Ofisoshin Jakadancinta Kimani 30 A Duniya
  • Bukatar Kawo Karshen Mamayar Da Kamaru Ke Yi Wa Yankunan Nijeriya
  • ’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista
  • An Yi Kira Ga Jihohi Da Su Kara Samar Da Ingantacciyar Hanyar Kiyon Lafiya
  • WTO Ta Yi Gargadi Akan Karin Kudin Fito Na Amurka
  • Araghchi: babu tattaunawa kan batun tace sinadarin uranium
  • Hamas ta bukaci hadin kan duniya domin kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza
  • Rasha ta ce tana bibiyar tattaunawar Iran da Amurka matuka
  • Kamfanonin Lantarki Na Shirin Shiga Yajin Aiki Kan Bashin Naira Tiriliyan 4
  • Amurka Tana Shirin Mikawa HKI Dubban Boma-Bomai Cikin Makonni Masu Zuwa