Iran Da Saudiyya Sun Tattauna Kan Taron OIC Mai Zuwa
Published: 27th, February 2025 GMT
Kasashen Iran da kuma Saudiyya sun tattauna kan halin da ake ciki a yankin dama batun taron kungiyar kasashen Musulmi ta OIC da za’ayi a cikin kwanaki masu zuwa a Jeddah.
Tattaunawar ta wakana ne ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan da Abass Araghchi, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran (RII).
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan halin da ake ciki a yankin, tare da tattauna taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar OIC da za a yi a Jeddah.
Dama a kwanan baya bangarorin sun tattauna kan shirin shugaban Amurka Donald Trump na kwace zirin Gaza dama tilasta wa falasdinawan yankin kaura zuwa Masar da Jordan, shirin da dukkan kasashen biyu sukayi fatali da shi.
Araghchi ya la’anci shirin na Amurka da ‘yan sahyoniya na tilastawa al’ummar Gaza komawa wasu kasashe a matsayin ci gaba da shirin ‘yan mulkin mallaka na shafe Falasdinu, yana mai jaddada bukatar daukar kwararan matakai na kasashen duniya don tunkarar wannan makirci.
Ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da sauran al’ummar duniya baki daya da su dauki matakin gaggawa kan lamarin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Da Ghana Sun Jaddada Aniyarrsu Wajen Kara Fadada Alakarsu A Dukkanin Bangarori
Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Ghana, John Mahama, sun tattauna batutuwa da dama domin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen yammacin Afirka.
An gudanar da ganawar ne a Abuja bayan da Mahama ya kai wa Tinubu ziyarar ban girma domin yabawa da halartar shugaban Najeriya a yayin bikin rantsar da shi a Accra, babban birnin Ghana.
Wannan dai ya zo ne watanni biyu bayan rantsar da Mahama bayan day a sake komawa kan karagar shugabancin kasar Ghana.
Daga cikin muhimman batutuwa da shugabannin kasashen na Najeriya da Ghana suka yi dubi a kansu, hard a yadda za a kara karfafa alakoki a dukkanin bangaroria tsakanin kasashen biyu.
Baya ga haka kuma sun tabo batun rarrabuwar kawuna da aka samua tsakanin mabobin kungiyar ECOWAS, da kuma matakan day a kamata a dauka domin dinke wannan baraka, da hakan ya hada hard a shiga tattaunawa da kasashen da suka balle suka kafa nasu kawancen, wato Nijar, Burkina Faso da kuma Mali, domin samun fahimtar juna da kuma yin aike tare domin ci gaban yankin da al’ummominsa.