Majalisar Dattijan Aljeriya Ta Soke Duk Wata Hulda Da Majalisar Dattijan Faransa
Published: 27th, February 2025 GMT
Majalisar Dattijan Aljeriya ta “dakatar da duk wata hulda da Majalisar Dattijan Faransa.
Majalisar al’ummar kasar, kwatankwacin majalisar dattijai a kasar Aljeriya, ta sanar da cewa ta “dakatar da dangantakarta” da majalisar dattawan Faransa, domin nuna adawa da ziyarar da shugabanta Gérard Larcher ya kai a ranakun Litinin da Talata a yankin yammacin Sahara.
Ziyarar ta biyo bayan wani gagarumin sauyi da shugaba Emmanuel Macron ya yi a watan Yulin shekarar 2024, inda ya nuna goyan baya ga shirin cin gashin kan yankin “karkashin ikon mulkin Moroko” wanda ya haifar da fushin Algiers.
Yankin da Spain ta yi wa mulkin mallaka na yammacin Sahara, wani yanki ne na hamada da Majalisar Dinkin Duniya ba ta yanke matsayi kansa ba, kashi 80% na kasar Maroko ne ke iko da shi, amma kungiyar ‘yan awaren Polisario, da ke samun goyon bayan Aljeriya, ta kwashe shekaru 50 tana fafatukar neman samun ‘yancinsa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dattijan da Majalisar
এছাড়াও পড়ুন:
Rikici ya ɓarke bayan wata mata ta mari ɗan sanda a Saudiyya
Hukumar ’Yan Sandan Saudiyya, ta yi magana kan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna wata mata tana mari wani ɗan sanda bayan ya hana ta wuce wata hanya da aka rufe.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta ce tana bincike domin tattara dukkanin bayanai kafin ɗaukar matakin da ya dace bisa doka.
Girgizar ƙasa ta hallaka sama da mutum 1000 a Myanmar Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a EdoBidiyon, wanda ya bayyana a ranar Juma’a, ya nuna matar tare da wata ƙawarta suna tunkarar wajen da aka kange, inda jami’an tsaro suka hana su wucewa.
Sai dai matar ta fusata, tare da marin ɗan sandan, shi ma daga bisani ya rama kafin wasu su shiga tsakani.
Lamarin ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke ganin matar ta ci zarafin jami’in tsaron yayin da yake bakin aikinsa.