Masar Ta Yi Watsi Da Shawarar Cewa Ta Karbi Ragamar Gaza Na Wucin Gadi
Published: 27th, February 2025 GMT
Masar ta yi watsi da shawarar da jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya gabatar na cewa Alkahira, maimakon kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta karbi ragamar zirin Gaza na wucin gadi, tana mai danganta irin wadannan tsare-tsare da cewa “ba za a amince da su ba.”
Kamfanin dillancin labarai na MENA ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen Masar Tamim Khalaf yana cewa, “Duk wani ra’ayi ko shawarwari da suka saba wa matsayar Masar da Larabawa (a kan Gaza) an yi watsi da su kuma ba za a amince da su ba.
Kakakin ya nanata kiran da Masar ta yi na janyewar Isra’ila daga yankunan Falasdinawa da ta mamaye, da kuma goyon bayanta ga kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.
Mista Khalaf ya jaddada “dangantaka ta zahiri” tsakanin Gaza, yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye da kuma gabashin al-Quds, yana mai cewa suna wakiltar “yankin kasar Falasdinu mai cin gashin kanta kuma dole ne su kasance karkashin cikakken ikon mallakar Falasdinawa da gudanar da mulki.”
A ranar Talata ne, Yair Lapid na Isra’ila ya gabatar da wani shiri na Gaza bayan kawo karshen yakin.
A karkashin shirin nasa, Masar za ta karbi ragamar tafiyar da yankin da zarar an kammala yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
“Mafita ita ce Masar za ta dauki nauyin gudanar da Zirin Gaza na tsawon shekaru takwas tare da zabin tsawaita shi zuwa shekaru 15,” kamar yadda ya shaida wa kungiyar Haukish Foundation for Defence of Democracy (FDD) a Washington.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Maduro Ya Bayyana Sakataren Harkokin Wajen Amurka Da Cewa Wawa Ne
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da yake ziyarar aiki a kasar Guyana da cewa, sakarai ne.
A yayin ziyarar da sakataren na harkokin wajen Amurka ya kai zuwa kasar Guyana mai makwabtaka da Venezuela, ya ce, Amurka za ta mayar da martani mai karfi akan Venezuela idan har ta kai wa Guyanan hari.
Rubio ya kara da cewa; Idan haka ta faru, to kuwa Venezuela za ta gwammace kida da karatu a wannan rana.
Amurkan dai ta kulla yarjejeniyar tsaro da kasar ta Guyana a yayin ziyarar da Rubio ya kai.
Shi kuwa shugaban kasar ta Venezuela da yake mayar da martani ya ce; Marco Rubio wawa, ya zo yana yi wa kasar Venezuela barazana daga kasar Guyana, sannan ya kara da cewa; Venezuela ta fi karfin a yi mata barazana, domin ita kasa ce ta ‘yanci.”
Alaka a tsakanin Venezuela ta Amurka ta sake tabarbarewa tun bayan da shugaba Donald Trump ya hau karagar mulki, bayan da ya kara kakaba mata takunkumai, da kuma batun mayar da ‘yan hijirar kasar daga Amurka.